Home Back

Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofarta Ga Kamfanonin Kasashen Waje

leadership.ng 2024/5/18
Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofarta Ga Kamfanonin Kasashen Waje

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da Elon Musk, shugaban kamfanin Tesla na kasar Amurka, mai kera motoci masu amfani da lantarki, jiya Lahadi a nan birnin Beijing, inda firaministan ya yi alkawarin kasuwar kasar Sin za ta kasance mai ci gaba da bude kofa ga kamfanoni masu jarin waje.

Yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana ci gaban da kamfanin Tesla ya samu a kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, yana mai cewa, hujjoji sun riga sun tabbatar da cewa, hadin gwiwa bisa adalci da moriyar juna, ya dace da ainihin muradun kasashen biyu, haka kuma ya cimma burikan al’ummominsu.

Firaministan ya kara da cewa, ana sa ran Amurka za ta hada hannu da kasar Sin wajen aiwatar da matsayar shugabannin kasashen biyu da kuma ci gaba da raya dangantaka mai karko a tsakaninsu, ta yadda za ta ci gaba da kawo alfanu ga jama’ar kasashen biyu da ma duniya baki daya.

Da yake bayyana kamfanoni masu jarin waje da gudunmuwarsu a matsayin wadanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban kasar Sin, firaministan ya ce, babbar kasuwar kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta gare su.

A nasa bangare, Elon Musk ya ce, katafariyar masana’antar Tesla dake Shanghai, ita ce mafi kokari cikin masana’antun kamfanin, kuma hakan ya samu ne saboda jajircewa da basirar ma’aikatanta Sinawa. Ya kuma ce, a shirye kamfanin Tesla yake ya ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da Sin tare da cimma sakamako na moriyar juna. (Fa’iza Mustapha)

People are also reading