Jigo a APC Ya Bayyana Abin da Ke Kokarin Wargaza Jam’iyyar a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Lukman Salihu ya nuna rashin gamsuwa kan yadda ake tafiyar da jam'iyyar a halin yanzu.
Lukman Salihu ya koka a kan cewa an riga an kaucewa dukkan dalilan da suka sa aka kafa jam'iyyar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lukman Salihu na cewa jam'iyyar APC ta dauki hanyar lalacewa saboda tana maimaita kurakuran da PDP ta yi a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lukman Salihu ya bayyana cewa a yanzu haka jam'iyyar APC ta fara nuna mulkin mallaka ga ƴaƴanta ta inda wasu ne kawai ke jan akalar jam'iyyar.
Ya ce ana tursasawa ƴaƴan jam'iyyar yan takara maimakon a bar su su zabi wanda suke so ya wakilci jam'iyyar.
Lukman Salihu ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta dauki halin da PDP ta yi a baya ta inda wadanda suka ci zabe ba sa biyayya ga uwar jam'iyya.
Jigon jam'iyyar ya kara da cewa jam'iyyar APC ta kaucewa dalilin kafata na magance matsalolin ilimi, kiwon lafiya da samar da walwala.
Lukman Salihu ya fadi cewa matsalar ta fara ne daga lokacin mulkin Muhammadu Buhari inda yake nuna kamar shi kadai ne zai iya tabuka komai a lokutan zabe.
Ya kuma kara da cewa sun yi tsammanin Bola Tinubu zai kawo gyara amma lamura sun kara taɓarɓarewa a mulkinsa, rahoton the Sun Nigeria.
Saboda lalacewar lamura, Lukman Salihu ya ce ba su gane yadda Tinubu ke tafiyar da mulkin ba, yana aiki kamar ba Tinubun da suka sani a baya ba.
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 17 na jihar Yobe.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wacce ta sanar da sakamakon zaɓen ta ce jam'iyyar ta lashe dukkanin kujerun ƙananan hukumomi.
Asali: Legit.ng