Home Back

Layya: Ko za a iya haɗa kuɗi a yi layya da dabba ɗaya?

bbc.com 2024/7/6
...

Asalin hoton, Getty Images

Layya ibada ce da al'ummar musulmi ke yi a cikin watan Zhul Hajji, wato wata na 12 na addinin musulunci sannan sunna ce ga Musulmin da ba su je aikin hajji ba ke yi a fadin duniya.

Ana yin layya ne a ranar 10 ga watan na Zhul Hajji, washegarin ranar Arfa wato ranar sallar idi babba.

Game da muhimmancin layya a addinin musulunci, Ustaz Hussaini Zakariyya, babban malami a cibiyar addinin Musulunci ta Usman bn Affan da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya ce,

"Layya wata ibada ce da musulmai suka gada daga annabi Ibrahim Alaihim Salam ta hanyar fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW). Ga duk wanda yake da iko zai yi yanka a ranar 10 ga watan Zhul Hajji ko ranar 11,12 da kuma 13 ga watan. "

Ya kuma ƙara da cewa layyar da Musulmi ke yi "wata jarabawa ce daga Allah (SWT) ta hanyar zubar da jini saboda shi. Ba don yana son jinin ko naman ba, sai don ya kankare wa bayinsa zunuban da suka yi."

Inda ya ƙara da cewa yin layyar sunna ce ta annabi Muhammad (SAW) domin shi ma ya yi kuma sahabbai sun yi a zamaninsa kuma ya yi umarni ga duk wanda yake da iko ya yi.

Mutanen da layya ta wajaba a kansu

...

Asalin hoton, Getty Images

Babban sharaɗin yin layya shi ne kasancewar mutum Musulmi sannan mai cikakken hankali, ba wanda ke da matsalar taɓin hankali ba.

Bayan cika waɗannan muhimman sharuɗɗa biyu malaman addinin musulunci sun yi karin haske kan waɗanda ya wajaba su yi layyar. kamar yadda Ustaz Zakariyya ya bayyana cewa.

"Waɗanda layya ta zama sunna a kansu su ne namiji ko mace, yaro ko babba, duk wanda ke da hali zai yi, domin ibada ce da ta game kowa da kowa."

Don haka a cewarsa iba da ce ta talaka da mai kuɗi, sarki da barorinsa, malami da almajiri, magidanci da matarsa kowa zai yi tasa layyar idan akwai halin yin hakan.

Nau'in dabbobin da ake layya da su

Wani abun da ya kamata mai niyyar yin layya ya yi la'akari da shi, shi ne, irin nau'in dabbobi da addinin musulunci ya amince a yanka domin yin layya.

Ana yin layya ne da dabbobin gida ba na daji ba ko da kuwa an yi kiwon na dajin ne a cikin gari ba a layya da su. Babban malamin ya yi karin haske kan ire-iren dabbobin da aka amince a yi layya da su.

"Ana layya da raƙumi na gida da saniya da raguna da tumakai da kuma awakai mazansu da matansu duka sun halatta a yi layya da su. "

Sai dai ya ce akwai sharaɗin cewa dole dabbobin su kasance masu lafiya ne kuma marasa tawaya, sannan su kasance suna da ƙiba gwargwadon samun mai a cikin namansu.

"Dabbobin su kasance suna da lafiya, ba sa ɗingishi, ba guragu ba, ba makafi ba ne, idan maza ne ƙahonsu bai karye ba, kunnensu bai yanke ba, basu rame ba sosai. To irin waɗanda basu da waɗannan abubuwa ya kamata a yanka a gabatarwa Allah (SWT) domin neman ladansa."

Sai dai malamin ya ƙara da cewa "amma an fi son yin layya da naman da ya fi daɗi don haka an fi son yi da ƙaramar dabba ya fi na babbar dabba daɗi don haka na rago ya fi na saniya, na saniya ya fi na raƙumi, don haka an fi son yin layya da ƙaramar dabba."

"Sai dai wanda ya fi lada ga mai aikin hajji (mai yin nau'in tumattu'i) an fi son ya yanka dabba mai yawan nama, soke raƙumi ya fi saniya, ita kuma ta fi rago da akuya." In ji Malam Zakariyya.

Babban malamin ya kuma yi karin haske kan cewa akwai wasu suffofin da ake son ragon da za a yi layya da shi ya samu, ko da yake mustahabbi ne ba dole ba ne.

Ana son ragon ya kasance yana da ƙiba yana da alamar mai kuma idan so samu ne ragon ya kasance yana da launi biyu. Baƙi da fari kuma baƙin launin ya zamanto shi ne a gaban jikin dabbar, farin daga bayanta.

Amma idan ba a samu ba kowanne irin launi aka samu za a iya yankawa.

Shin za a iya yin layyar haɗaka?

Ustaz Hussaini Zakariyya ya bayyana cewa mutane za su iya haɗa kuɗi su sayi dabba guda domin yin layya da ita, wato layyar haɗaka.

Sai dai ba a yin hakan a kan ƙaramar dabba kamar rago, tunkiya, akuya ko bunsuru. Ana layyar haɗaka ne kawai a kan shanu da raƙuma.

Mutum biyar ko bakwai na iya haɗa kuɗi su sayi saniya ko raƙuma su yanka.

"Haka kuma idan mutum ya yanka abin da zai yanka, ya halalta ya ajiye naman shi kadai ya ci ba tare da ya bayar da sadaka ko kyauta ba.

Sannan zai iya sadaka ko kyautar naman gaba ɗaya ba tare da ya ci komai ba, ko ya raba naman gida biyu ya ci rabi ya bayar da kyauta ko sadakar rabin. Ko kuma ya raba naman gida uku ya ci ya bayar sadaka da kuma yi kyauta. An ba da damar yin haka a shari'ar musulunci." In ji babban malamin.

Ko layya ta wajaba kan matasa marasa aure?

A ƙarƙashin shari'ar Musulunci ya halatta mace ko namiji marasa aure, amma kuma suna da hali su ma za su yi layyar.

"Yaron da ya ke da dukiya kuma yake da waliyyai masu kula da dukiyarsa za su iya ɗaukar wani yanki na dukiyar su yi masa layya. Bare kuma samari ko ƴanmata da watakila suke aiki ko suke makaranta amma suna da kuɗinsu za su iya layya, ba sai masu aure ne kaɗai ke layya ba." In ji Ustaz

Haka zalika ya shehun malamain ya ce ya halasta a cewarsa iyaye su yanka wa ƴaƴansu baki ɗaya ko kowannensu a yi masa nasa ko da ba zai ci ba.

"Wato a nema masa kusanci ga Allah (SWT) domin idan yaro ƙarami ya yi ibada mahaifansa ne suke da ladan domin shi ba a fara rubuta masa lada ba ko zunubi." Kamar yadda ya ƙara haske.

People are also reading