Home Back

Gwamnatin Tinubu Ta Gargadi Ma'aikata Ana Dab da Fara Yajin Aiki

legit.ng 2024/6/26
  • Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ma'aikata dangane da shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka shirya fara gudanarwa a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni
  • Ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa ma'aikatan da suka shiga cikin yajin aikin za su iya fuskantar hukuncin ɗauri a gidan yari
  • Ministan ya bayyana cewa yajin aikin ya saɓa doka saboda ƙungiyoyin ƙwadagon ba su ba da sanarwar shiga yajin aikin ba kwanaki 15 kafin farawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ma’aikatan da ke shirin shiga yajin aikin sai baba ta gani da ƙungiyoyin ƙwadago suka ayyana.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za su iya fuskantar ɗaurin watanni shida a gidan gyaran hali.

Gwamnatin tarayya ta gargadi ma'aikata kan yajin aiki
Gwamnatin ta gargadi ma'aikata kan shiga yajin aikin kungiyoyin kwadago Hoto: Emmanuel Osodi/Majority World/Universal Images Group, Krisztian Bocsi/Bloomberg Asali: Getty Images

Antoni Janar kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lateef Fagbemi ya ce sashe na 18 na doka ya buƙaci ma’aikacin da ke aiki a wurare masu muhimmanci da ya sanar da wanda ya ɗauke shi aikin kwanaki 15 kafin ya daina aiki.

Ya ce duk wanda bai yi hakan ba zai fuskanci hukuncin tara ko ɗaurin watanni shida.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta daɗe tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a cikin kwamitin samar da mafi ƙarancin albashin, domin fito da sabon abin da za a riƙa biyan ma'aikata kuma ba ta ayyana kawo ƙarshen tattaunawar ba.

Ministan ya ci gaba da cewa yajin aikin da ake shirin yi ya saɓawa umarnin kotun masana’antu ta ƙasa da kuma ƙoƙarin sasantawa da masu shiga tsakani ke yi kan batutuwan da suka shafi mafi ƙarancin albashin.

Asali: Legit.ng

People are also reading