Home Back

Batun Biyan Dubu ₦105 Ƙazon Kurege Ne – Fadar Shugaban Ƙasa

leadership.ng 2024/6/26
Batun Biyan Dubu ₦105 Ƙazon Kurege Ne – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata ikirarin cewa ministan kuɗi Wale Edun ya miƙa ƙudirin biyan mafi ƙarancin albashi na ƙasa N105,000 duk wata ga shugaban ƙasa Bola Tinubu. Wannan musantawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce musamman bayan da shugaba Tinubu ya baiwa Edun wa’adin sa’o’i 48 domin ya gabatar da kudurin biyan mafi karancin albashin ma’aikata, biyo bayan wani yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC suka gudanar a faɗin ƙasar.

Jita-jitar dai ta nuna cewa tuni Edun ya gabatar da shirin mafi ƙarancin albashi ga shugaban ƙasa. Sai dai mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi ƙarin haske a shafukan sada zumunta cewa babu wata shawara da aka bayar kan adadin kuɗin. Ya jaddada cewa rahotannin da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama.

Wannan bayanin ya yi daidai da ƙoƙarin da Gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi na tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadagon don magance buƙatunsu, gami da gyara ga mafi ƙarancin albashi na kasa.

Gwamnatin ta mayar da hankali ne a kan samar da ingantacciyar hanyar da za ta magance matsalolin tattalin arzikin ma’aikata ba tare da haifar da wani cikas ga al’umma ba.

Shugaban ƙasa

People are also reading