Home Back

Kaduna: An Shiga Tashin Hankali Yayin da Wata Amarya Ta Datse Mazakutar Angonta

legit.ng 2024/6/29
  • An shiga tashin hankali a garin Kudan da ke jihar Kaduna, bayan wata amarya ta yanke mazakutar angonta yana barci
  • An ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Mayu, kuma angon mai suna Salisu Idris na kwance a asibiti yana jinyar raunin
  • Salisu ya bayyana kaduwarsa kan aika-aikar da amaryarsa Habiba Ibrahim ta yi a kansa duk da babu wani sabani a tsakanin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Wani lamari mai ban mamaki ya faru a jihar Kaduna, inda wata amarya mai suna Habiba Ibrahim ta gurfana a gaban kotu bisa zargin cin zarafin mijinta, Salisu Idris.

An ruwaito cewa Habiba Ibrahim ta yi amfani da wuka mai kaifi ta yanke mazakutar angonta Salisu Idris a lokacin da ya ke tsakiyar barci.

An gurfanar da amarya a gaban kotu a Kaduna
Kaduna: Wata amarya ta yanke mazakutar angonta yana barci. Hoto: Legit.ng Asali: Original

Lamarin wanda ya afku a ranar 26 ga watan Mayu, ya jefa al’umma cikin rudani yayin da angon ke kwance rai hannun Allah, in ji rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amarya ta farmaki angonta yana bacci

Salisu Idris, dan shekara 40 mai yin sana'ar acaba a garin Kudan, Jihar Kaduna, ya ba da labarin abin da ya faru da kuma yadda ya tsira da rayuwarsa.

Ya bayyana cewa:

"Na dawo gida daga sallar Asubah, na dan kwanta domin na huta, a lokacin ne ta farmake ni da wuka mai kaifi, ya datse mazakuta ta.
"Ba domin Allah ya sa makota sun jiyo ihu na sun kawo mun dauki cikin gaggawa ba, da sai dai ayi wani labarin kuma ba wannan ba."

Salisu da Habiba na kaunar juna

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa akwai kauna mai karfi tsakanin angon da amaryar, kuma duka-duka watanni hudu kenan da yin auren su.

Ango Salisu ya bayyana kaduwarsa kan wannan mummunar aika-aika da matar ta yi a kansa yana mai cewa babu wani sabani da ya shiga tsakanin su a iya sanin sa.

An ruwaito cewa an garzaya da angon asibitin Kudan bayan faruwar lamarin, daga can aka tura shi babban asibiti na Makarfi.

Yadda ake ciki game da lafiyar Salisu

Wata majiya ta ce an kuma garzaya da Salisu asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya ke kwance a bangaren A na dakin maza da aka yi wa tiyata.

A halin yanzu dai Salisu na murmurewa daga wannan ta'adin da matar ta yi masa wadda ita ma aka tabbatar tana dauke da juna biyu.

Babban abin da ya fi ba mutane mamaki game da faruwar lamarin shi ne yadda matar ta yi amfani da wukar da angon ya wasa ta da kansa a daren faruwar lamarin.

'Yan kwadago sun janye yajin aiki

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na Najeriya sun janye yajin aikin gama gari da suka shiga bayan tattaunawarsu da gwamnatin tarayya.

Kungiyar kwadago na NLC da TUC sun ce sun tsagaita da yajin aikin ne na mako guda kadai, inda za su saurari bangaren gwamnatin ko za ta iya biyan bukatarta kan mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

People are also reading