Home Back

Bama goyon bayan ƙirƙiro ƴan sandan jahohi dan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasa – Human Rights

dalafmkano.com 2024/5/21

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce akwai buƙatar duba na tsanaki gabanin sahale ƙirƙirar ƴan sandan jahohi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a yau Talata.

Galadanci, ya kuma ce duba da a mafi yawan lokuta ake samun baragurbi a harkar samar da taro, kamata ya yi a wadata jami’an tsaron da ake da su da kayan aiki na zamani, ta yadda za’a ƙara musu Gwiwa akan aikin su.

“A ɓangaren ƙungiyar mu bama goyon bayan samar da ƴan sandan jahohi, domin hakan ka iya haifar da koma baya; kuma ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a sassan ƙasar nan, “in ji shi”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya da ta jahohi, su kula da al’ummar su tare da samar musu kayayyakin more rayuwa, dan rayuwar su ta tafi yadda ya kamata.

People are also reading