Home Back

‘Yansanda Sun Gurfanar Da ‘Yan Daba 104 A Kano

leadership.ng 2024/5/13
Gaskiya Ta Bayyana Game Da Bullar Mata Masu Shan Jini

Rundunar ‘yansndan Jihar Kano ta gurfanar da mutum 104 da ake zargi ‘yan daba ne a gaban wasu kotuna da ke unguwar Nomandsland a Jihar.

An kama mutanen a wuraren hawan sallah da masarautun Kano ke yi duk shekara a bukukuwan sallah.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce ana zargin mutanen da laifukan daba da rike makamai da kuma ta’amali da miyagun kwayoyi.

Kiyawa, ya ce an samu kama mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan rundunar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.

A baya-bayan nan ma rundunar ta Kano ta kama wasu da ta ce ‘yan daba ne wadanda kuma suke addabar unguwar Dorayi.

People are also reading