Home Back

Kano: NNPP Ta Gano Makarkashiyar APC Domin Hana Mulkin Gwamna Abba Samun Nasara

legit.ng 2024/7/3
  • Yayin da ake cikin rigimar sarautar Kano, jam'iyyar NNPP ta bayyana waɗanda ke neman ruguza jihar Kano a Arewacin Najeriya
  • Jam'iyyar ta zargi APC da neman kawo rudani a jihar domin kwace mulkin jihar karfi da yaji kuma ta kowace hanya
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Gwamnatin Tarayya da shiga rigimar jihar wajen amfani da bangaren shari'ar da jami'an tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta zargi APC da neman kawo rudani a jihar Kano.

Jam'iyyar ta zargi APC mai mulki da neman kwace mulkin jihar Kano ta kowace hanya wajen kawo rudani.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ta kasa, Ladipo Johnson ya fitar a ranar Laraba 19 ga watan Yunin 2024, cewar Vanguard.

Johnson ya ce APC na neman kifar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf karfi da yaji wajen kawo rudani a jihar.

Ya ce yadda APC ta yi kane-kane a rigimar sarautar Kano hakan ya nuna damuwarta wurin kwace mulkin Kano ta kowace hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"APC ba su taba boye maitarsu ta neman rikita Kano da kwace ikon halastaccen Gwamna Abba Kabir ba."

- Ladipo Johnson

Jami'yyar ta ce APC na amfani da bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro domin kawo rudani a jihar.

Ta bukaci ƴan Najeriya da su tashi tsaye kan wannan makirci da APC ke ƙullawa da ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Kwankwaso ya zargi Tinubu kan rigimar Kano

A wani labarin mai kama da wannan, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarautar Kano.

Kwankwaso ya ce Bola Tinubu yana kokarin kawo rudani a jihar domin sanya dokar ta ɓaci da kwace mulkin Kano.

Daga bisani, Bola Tinubu ya musanta zargin da Kwankwaso ya ke yi kan gwamnatinsa inda ya ce babu kamshin gaskiya a maganar.

Asali: Legit.ng

People are also reading