Kano: NNPP Ta Gano Makarkashiyar APC Domin Hana Mulkin Gwamna Abba Samun Nasara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta zargi APC da neman kawo rudani a jihar Kano.
Jam'iyyar ta zargi APC mai mulki da neman kwace mulkin jihar Kano ta kowace hanya wajen kawo rudani.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar ta kasa, Ladipo Johnson ya fitar a ranar Laraba 19 ga watan Yunin 2024, cewar Vanguard.
Johnson ya ce APC na neman kifar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf karfi da yaji wajen kawo rudani a jihar.
Ya ce yadda APC ta yi kane-kane a rigimar sarautar Kano hakan ya nuna damuwarta wurin kwace mulkin Kano ta kowace hanya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"APC ba su taba boye maitarsu ta neman rikita Kano da kwace ikon halastaccen Gwamna Abba Kabir ba."
- Ladipo Johnson
Jami'yyar ta ce APC na amfani da bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro domin kawo rudani a jihar.
Ta bukaci ƴan Najeriya da su tashi tsaye kan wannan makirci da APC ke ƙullawa da ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
A wani labarin mai kama da wannan, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarautar Kano.
Kwankwaso ya ce Bola Tinubu yana kokarin kawo rudani a jihar domin sanya dokar ta ɓaci da kwace mulkin Kano.
Daga bisani, Bola Tinubu ya musanta zargin da Kwankwaso ya ke yi kan gwamnatinsa inda ya ce babu kamshin gaskiya a maganar.
Asali: Legit.ng