Home Back

Harin ta'addanci ya halaka jami'an gwamnatin Nijar da soja

dw.com 2024/7/6
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Wani harin kwanton bauna ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar 3 da kuma soja guda daya da ke musu rakiya, a kan iyakarta da Najeriya, kamar yadda rundunar sojin Nijar din ta sanar.

Jami'an dai na kan hanyarsu ta zuwa Diffa da ke Kudu maso yammacin Nijar, inda maharan suka tsallako daga Najeriya suka harbe su.

Diffa da ke da iyaka da kasashen Kamaru da Chadi da kuma Najeriya, na fama da hare-haren 'yan Boko Haram tun a shekarar 2015.

People are also reading