Home Back

Akpabio ya shirga ƙarya, Naira biliyan 2 kacal Tinubu ya ba kowace jiha, ba Naira biliyan 30 ba – Gwamna Makinde

premiumtimesng.com 2024/4/28
Akpabio ya shirga ƙarya, Naira biliyan 2 kacal Tinubu ya ba kowace jiha, ba Naira biliyan 30 ba – Gwamna Makinde

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya maida wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio zazzafan raddi, bayan Akpabio ya ce gwamnatin tarayya ta raba wa gwamnoni kowane Naira biliyan 30, domin ya raba wa talakawa tallafin abinci.

Makinde ya ƙaryata Akpabio a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da katafaren masallacin biliyoyin kuɗaɗe a garin Iseyin.

Gwamnan Oyo ya ce bai kamata mutum na uku a muƙami a Najeriya ya riƙa kantara wa ‘yan Najeriya ƙaryar rashin kunya ba.

Ya ce ya cika da mamaki da ya ji Akpabio ya furta cewa shi ma labari aka ba shi, bai tabbatar ba.

“To a gaskiya matsawar shugaba kamar na Majalisar Dattawa a ce ya na fitowa ya na ƙadda-ƙanzon-kurege kan maganar da bai tabbatar ba, wannan siyasa ce mai haɗari.”

Makinde ya ce bai kamata a riƙa siyasantar da mummunan halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.

Ya ce a matsayin sa na Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, shi dai ba wanda ya ba shi ko Naira 1 ballantana Naira biliyan 30.

“Kuma na san dukkan sauran gwamnonin ba wanda aka ba ko sisi.

“Abin da kawai kowa ya sani a Najeriya shi ne, cikin watan Satumba Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bai wa kowace jiha ramcen Naira biliyan 5 domin ta tallafa wa talakawa. Daga cikin kuɗin an bai wa kowace jiha Naira biliyan 2. Tun Satumba, amma har yau ba a cika mana sauran Naira biliyan 3 ba.

“Sannan kuma yanzu haka ana ta damun mu cewa mu biya Naira biliyan 2 ɗin da aka ba mu ramcen, tun ma kafin a cika mana sauran Naira biliyan 3 ɗin.

“Ya kamata duk mai hankali ya sani cewa babu yadda za a yi Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta bai wa gwamnoni kuɗi. Wannan ma ba zai yiwu kamar yadda Akpabio ya ce ya ji labari ba.”

Daga nan Makinde ya yi kira ga Akpabio cewa ya guji yin kalaman siyasantar da lamari musamman na matsalar tsadar rayuwa.

Ya ƙara da cewa haƙƙin gwamnatin tarayya ne ta tashi haiƙan ta fitar da ƙasar nan cikin mawuyacin halin da ta jefa ta a ciki.

Kalaman Akpabio Da Suka Janyo Aka Yi Masa Zazzafan Raddi:

”An Ce Kowane Gwamna Ya Karɓi Naira Biliyan 30 Daga Tarayya, Domin Raba Wa Talakawa Abinci’ – Sanata Akpabio:

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi iƙirarin cewa ya samu labarin da bai tabbatar ba cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowane gwamna kuɗin kishi-kishi, har kowa ya karɓi Naira biliyan 30, domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa.

Akpabio ya bayyana cewa an ciri kuɗin ne daga Asusun Gwamnatin Tarayya an raba wa gwamnonin domin a rage tsadar kayan abinci da tsadar rayuwa a kowane jiha.

Akpabio ya bayyana haka a zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata, inda ya ce labarin da ya zo masa na nuni da cewa an ba su kason farko ba tun yau ba, sannan kuma gwamnonin dai sun sake karɓar Naira biliyan 30 kowanen su daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

“Tilas ta kama zan bayyana cewa kowace jiha ta karɓi Naira biliyan 30 cikin ‘yan watannin nan daga Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).

“Waɗannan kuɗaɗe da aka ba su, ba su cikin haƙƙin kuɗaɗen su da gwamnatin tarayya ke ba su na duk ƙarshen wata daga Asusun Gwamnatin Tarayya. An ba su ne domin su rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci,” cewar Akpabio.

Akpabio ya shawarci gwamnoni su yi amfani da kuɗaɗen ta inda ya dace, kuma ta hanyar amfana su ga talakawa da marasa galihu, domin rage masu tsadar rayuwa.

“Mun yi amanna da cewa matsawar gwamnoni za su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar wadatar da abinci, to za a samu sauƙi sosai.

“Gwamnatin jiha na da jan aiki a kan ta. Ita ce kusa da jama’a. Ba na so na ce ƙananan hukumomi ne suka fi kusanci da jama’a, domin kowace ƙaramar hukuma a yanzu ƙarƙashin gwamna take.

“Amma dai na yi amanna cewa idan gwamnatin jiha za ta yi abin da ya kamata, to sai ta jawo ƙananan hukumomi wajen raba kayan abincin ga mabuƙata.” Inji Akpabio.

Akpabio ya yi wannan iƙirarin daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da ɗanɗana raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci.

Tuni ake ta samun rahotannin zanga-zanga a jihohi daban-daban.

Ita kuwa Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NL ), ta sanar cewa a ranakun 27 da 28 ga Fabrairu za a yi zanga-zangar game-gari a faɗin ƙasar nan.

 
People are also reading