Home Back

“An Yi Hawan Sallah da Shi”: Masarautar Zazzau Ta Yi Babban Rashi, Yarima Aminu Ya Rasu

legit.ng 2024/5/17

Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa masarautar Zazzau ta yi rashin Yarima kuma Hakimi, Injiniya Aminu Umar.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Marigayin ya rasu ne bayan ya halarci dukkannin bukukuwan Sallah da suka hada da hawan Daba da sauransu kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Marigayi Injiniya Umar wanda kuma shi ne Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, yana daga zuriyar marigayi Sarki Dalhat daga tsatson Barebari da suka mulki masarautar Zazzau.

Ya taba zama shugaban hukumar ruwa ta jihar Kaduna.

A matsayinsa na Walin Zazzau, marigayi Injiniya Umar yana daya daga cikin manyan masu rike da mukamai a masarautar.

A wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar, ya tabbatar da rasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Aliyu Kwarbai ya ce marigayin ya halarci bikin Hawan Daushe da na Daba da aka yi a Zariya a ranar Juma’a.

Ya kuma ce yana daya daga cikin hakimai da suka kai wa Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli gaisuwar Sallah.

Asali: Legit.ng

People are also reading