Home Back

Alhazan Kano Sun Cikin Alheri, An Fara Ba Su Abinci da Kulawa da Lafiya Kyauta a Saudiyya

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamnatin jihar Kano ta fara ciyar da alhazan jihar sau biyu a kowace rana a masaukinsu da ke ƙasar Saudiyya
  • A wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamna, Shu'aibu Ibrahim, ya fitar ya ce gwamnati ta tura kwararrun likitoci su kula da maniyyatan Kano
  • Har ila yau gwamnatin ta tura tawagar kula da mahalli waɗanda za su tabbatar da aminci da tsaftar masaukin alhazan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Gwamnatin jihar Kano ta ce tana baiwa alhazan jihar da a halin yanzu suke kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana na 2024 abinci kyauta sau biyu a kullum.

Mai magaba yawun alhazan jihar Kano kuma kakakin mataimakin gwamnan jihar, Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Alhazai a Masallacin harami.
Gwamnatin Kano tana ciyar da alhazai sau biyu a kowace rana a Saudiyya Hoto: Inside The Haramain Asali: Facebook

Ya ce gwamnati ta fara ciyar da alhazan ne domin tabbatar da walwala da jin dadinsu a tsawon lokacin da za su shafe a ƙasa mai tsarki, jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya kara da cewa ana bayar da abincin sau biyu a rana ga daukacin alhazan jihar Kano, ba tare da la’akari da matsayinsu ko dukiyarsu ba.

Abincin, wanda tawagar ƙwararrun masu dafa abinci ke girkawa, sun haɗa da masu gina jiki da daɗi, kuma ana yin su ne a cikin tsafta muhalli mai tsafta,” in ji shi.

Baya ga abincin, gwamnatin jihar Kano ta kuma tura tawagar kwararrun likitocin kasar Saudiyya domin kula da lafiyar alhazai.

Tawagar likitocin da ta hada da likitoci, ma’aikatan jinya, da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya, tana sansanin alhazai na jihar Kano da ke Makkah.

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta kuma tura tawagar kula da muhalli domin tabbatar da aminci da tsaftar muhallin mahajjata.

"Alhazai da masu ruwa da tsaki sun yaba, inda suka yabawa gwamnati bisa jajircewar da ta yi wajen kyautata rayuwar al’ummarta a kasa mai tsarki,” in ji sanarwar.

A wani rahoton kuma

Asali: Legit.ng

People are also reading