Home Back

TA FARU TA ƘARE: Majalisar Dokokin Edo ta tsige Shaibu, Mataimakin Gwamna

premiumtimesng.com 2024/5/19
Gwamnatin Edo za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 200

Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige Mataimakin Gwamna, Philip Shaibu, a ranar Litinin.

Tsige shi ya biyo bayan yin amfani da shawarwarin da Kwamitin Bincike mai mambobi 7 ya gabatar wa Majalisa, wanda ke ƙarƙashin tsohon Mai Shari’a Mai Ritaya, Stephen Omonua.

A zaman Majalisa na yau Litinin a Benin babban birnin Jihar Edo, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisa, Charity Aigoubarueghian, ta ce rahoton kwamitin bincike ya samu Shuaibu da laifin bayyana sirrin gwamnati.

Ta kuma ce duk da kwamitin bai ayyana laifin cin amana da ƙarya ga jihar Edo ba, amma kwamitin ya gano batutuwa biyu, sai kuma shawara ɗaya wadda daga shawarar ce batun tsige Mataimakin Gwamna ɗin ta taso.

Ya ce, “Kwamitin Bincike mai mambobi bakwai ya bada shawarar a tsige Mataimakin Gwamna, saboda dalilin laifin bayyana sirrin gwamnati da ya yi.”

Yayin da ake neman amincewar ‘yan Majalisa kafin a tsige shi, 18 daga cikin 19 ɗin da suka halarci zaman duk sun amince a tsige shi. Guda ɗaya ne kaɗai bai tsaya an yi zaɓen da shi ba.

Magatakardar Majalisa, Yahaya Omogbai, shi ne ya miƙe tsaye ya ƙidaya waɗanda suka ɗaga hannun goyon bayan tsigewa.

Daga nan ya ce tsigewar ta tabbata, domin an cika sharuɗɗan da doka gindaya, wato aƙalla a samu kashi 2/3 na yawan ‘yan Majalisa su amince.

Gwamna Obaseki ya ci zaɓen farko a ƙarƙashin APC. Rigimar sa tsohon Shugaban PDP na Ƙasa, kuma tsohon Gwamnan Edo ce ta sa shi da mataimakin sa suka canja sheƙa zuwa PDP, kuma suka ci zaɓe a zango na biyu.

Kakakin Majalisa, ya umarci Magatakarda ya gabatar da kwafe-kwafen tsige Mataimakin Gwamna ga Gwamna Godwin Obaseki.

People are also reading