Home Back

Hajjin 2024: Gwamna a Arewa Ya Ba Maniyyatan Jiharsa Tallafin Makudan Kudi

legit.ng 2024/5/10
  • Yayin da ake korafi kan karin kudin kujerar aikin hajji, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ba da tallafi mai tsoka
  • Gwamna ya dauki nauyin biyan N1m ga maniyyatan da suka fara biyan kudin kujerar kafin kara kudin da hukumar ta yi
  • Kakakin hukumar alhazai a jihar, Usman Murtala shi ya bayyana haka a yau Litinin 1 ga watan Afrilu a birnin Dutse

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ragewa maniyyata N1m a cikin kudin kujerar hajji.

Gwamnan ya yi hakan ne bayan hukumar alhazai ta kara kudin kowace kujera da N1.9m a makon da ya wuce.

Gwamnan Arewa ya gwangwaje maniyyata da tallafin kudin kujerar hajji
Gwamna Umar Namadi ya ba maniyyata kyautar N1m a Jigawa. Hoto: Umar Namadi. Asali: Facebook

Wadanda za su ci gajiyar daga maniyyata

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar alhazai jihar, Usman Murtala ya fitar a yau Litinin 1 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murtala ya ce tallafin na maniyyata ne a jihar da suka fara biyan kudin kujerar aikin Hajj, cewar Premium Times.

"Kowane maniyyaci yanzu zai biya N900,000 madadin N.19m da hukumar alhazai ta kara a kwanakin baya."
"Tun farko, hukumar ta ware kujeru 1,518 ga maniyyata a jihar amma 1,260 ne kadai aka fitar wadanda suka kammala biyan kudin."

- Usman Murtala

Usman ya ce wannan tallafi zai shafi wadanda suka fara biyan kudin ne kafin hukumar ta kara kudin kujerar zuwa N1.9m., cewar Daily Trust.

Musabbabin karin kudin kujerar hajji

Wannan na zuwa ne bayan ƙarin kudin kowace kujera da hukumar alhazai ta yi na N1.9m a makin da ya gabata.

Hukumar ta fadi dalilan karin da suka hada da yanayin tashin farashin dala da sauran matsaloli a kasar.

Kaura ya biya rabin kudin kujerar hajj

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tallafawa dukkan alhazan jiharsa.

Gwamna Muhammed ya amince zai biya kaso 50 na karin ga kowane mahajjaci na jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan ƙarin kudin kowace kujera da hukumar alhazai ta yi na N1.9m a makin da ya gabata.

Asali: Legit.ng

People are also reading