Home Back

Hare-haren boma-bomai sun yi ajalin mutane a Najeriya

dw.com 2024/7/7
Hukumomin tsaro a wajen tashin Bom a jihar Borno a Najeriya
Hukumomin tsaro a wajen tashin Bom a jihar Borno a Najeriya

Wasu hare-haren boma-bomai da aka kai wajen bikin aure da kuma wajen jana'iza a jihar Borno, sun salwantar da rayukan mutane da dama galibi mata da matasa da kuma kananan yara.

Lamarin ya faru ne a garin Gwoza da ke kudancin jihar, inda wasu ma fiye da mutum 100 suka jikkata.

Wadanda suka shaida lamarin da ya faru a jiya Asabar, sun ce bam na farko ya tashi ne a wurin bikin auren inda ake zargin wata matar da ta gabatar da kanta a matsayin mai bara ta tayar.

Na biyu kuma ya tashi ne a wajen da ake jana'izar daya daga cikin wadanda bam na farko ya hallaka.

'Yansanda sun ce mutum takwas ne suka mutu, amma wasu shaidun na cewa adadin ya zarta haka.

People are also reading