Home Back

Marafa Ga Matawalle: Girmama Tinubu Ba Matsalar Nijeriya Ba Ce

leadership.ng 2024/5/20
Marafa Ga Matawalle: Girmama Tinubu Ba Matsalar Nijeriya Ba Ce

Jigon jam’iyyar APC, Sanata Kabiru Marafa ya caccaki karamin ministan tsaro, Bello Matawalle wanda ya siffanta kungiyar dattawan arewa a matsayin matsalar siyasar arewa. 

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Marafa ya bayyana wa Matawalle cewa kungiyar dattawan arewa ba juji ba ne, ya bukaci ministan ya janye kalamunsa cikin gaggawa tare da neman afuwar kungiyar dattawan arewa da kuma mutanen arewa gaba daya.

Shi dai Matawalle ya bayyana cewa, a gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Tinubu, kungiyar dattawan arewa ta kasance matsalar siyasar arewa wanda ba ta magana da yawun yankin, sannan ya siffanta kungyar da juji.

Marafa ya kasance ko-odineta na kungiyar yakin neman zaben Tinubu/Shettima a 2023 a Jihar Zamfara, ya ce maimakon Matsawalle ya yi kalamun suka game da kungiyar dattawan arewa, ya kamata ya lissafo nasarori da manufofin gwamnatin Tinubu a arewa da ma kasa baki daya a farkon watanni 10 a wannan gwamnati.

A cewarsa, dattawan arewa sun bayar da gudummuwa wajen samun yawan kuri’u ga gwamnatin Tinubu wajen kokarin ya magance matsalolin tsaro da yanki ke fuskanta da ayyukan ta’addanci da farfado da tattalin arziki da kuma inganta kayayyakin more rayuwa.

Ya ce lallai Tinubu yana bukatar goyon bayan dattawan arewa wajen cika manufofinsa a kasar nan.

Sai dai kuma, wasu kungiyoyin matasa daga arewacin Nijeriya sun ce kokarin da Sanata Marafa yake nunawa na kare dattawan arewa na NEF ba komai ba ne illa haddasa husuma a tsakanin shugaban kasar da mutanen arewa. Sun fadi haka ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja bisa jagorancin shugabannin kungiyoyin, Kabiru Yusuf Godiya da Yahaya Garba.

People are also reading