Home Back

ZARGIN KASHE ƊAN MAJALISA: Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Takum ya taka a guje, yayin da mai shari’a ya bada sammacin damƙo shi

premiumtimesng.com 2024/5/17
Police_officer_chase
Police_officer_chase

Shari’ar zargin kisan Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Taraba ta ɗauki ‘yan kallo a ranar Alhamis, bayan da Mai Shari’a ya bayyana sammacin umarnin kamo tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Takum, Shiban Tikari, wanda ya taka a guje.

Ana zargin Shiban Tikari da hannu a kisan ɗan majalisar dokoki Hosea Ibi.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Taraba, David Iloyanomon ne ya bayyana haka ga manema labarai, ranar Alhamis, a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Iloyanomin ya ce Babban Cif Jojin Jihar Taraba ne ya bada umarnin a kamo Tikari, wanda ya taka da gudu ba a san inda ya ɓoye ba.

“Dama mu mun nuna tsoron mu da damuwa, ganin yadda Cif Joji zai bayar da umarni a bayyane cewa a kawo Tikari. Amma dai dukkan mu mun fito fafutikar tabbatar da mun yi nasarar kamo shi.

“Muna farautar sa. Ba a daɗe ba mun samu labarin cewa ya fice daga jihar. Amma za mu damƙo shi a duk inda ya ke, za mu gabatar da shi domin a yi masa hukunci.”

Wanda aka kashe ɗin dai shi ne wakilin Takum 1. An yi garkuwa da shi tun a ranar 30 ga Disamba, 2017, a gidan sa tsallaken Ada Barracks, cikin Takum.

An tsinci gawar sa bayan kwanaki 16 da sace shi, a kan titin Takum Kashimbila, a Ƙaramar Hukumar Takum.

An kama waɗansu da ake zargi, aka gurfanar da su Babbar Kotun Jalingo, inda suka bayyana cewa Tikari ne ya ɗauko hayar su domin su kama ɗan majalisar su yi garkuwa da shi.

People are also reading