Home Back

Mummunan Gobarar Dare Ta Tashi a Kasuwar Abuja, an Gargadi Mazauna Yankin Karu

legit.ng 6 days ago
  • A yammacin yau Alhamis, 27 ga watan Yunin 2024 ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja
  • An ruwaito cewa gobarar ta kama gadan-gadan yayin da jami'an hukumar kwana-kwana ke iya bakin kokarinsu domin shawo kanta
  • Wani bidiyo ya nuna yadda gobarar take ci a kasuwar inda aka yi kira ga mazauna yankin da su guji taruwa a wajen da wutar ta tashi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa wuta ta kama a kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja, inda take ci har yanzu.

Gobarar wadda ta tashi a yammacin ranar Alhamis, ta mamaye shaguna da dama yayin da take ci gadan-gadan.

Abuja: A halin yanzu kasuwar Karu na ci da wuta.
Gobara ta tashi a kasuwar Karu da ke Abuja. Hoto: @Fedfireng Asali: Facebook

Gobara ta tashi a kasuwar Karu, Abuja

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa har zuwa karfe 8:00 na dare jami'an hukumar kashe gobara na kokarin shawo kan wutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya shaida cewa an kira jami'an hukumar kwana-kwana domin ganin gobarar ba ta tsallaka gidajen makota ba.

Har zuwa yanzu dai ba a gano musabbabin tashin wutar ba yayin da hukumomi ke kira ga mazauna yankin da su guji taruwa a inda wutar ta tashi.

A cewar wani bidiyo da @Abujaplug ya wallafa a shafinsa na X, ya ce "kasuwar Kauru ta kama da wuta."

Kalli bidiyon a ƙasa:

Asali: Legit.ng

People are also reading