Home Back

Wani gungun shugabannin mazaɓar Ganduje sun ƙara lafta wa Ganduje takardar ‘dakatarwa’ daga APC

premiumtimesng.com 2024/5/19
Ganduje Umar
Ganduje Umar

Wani gungun shugabannin APC da suka ɓalle daga mazaɓar Ganduje cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, sun ayyana ƙara tafta wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kuma Shugaban APC na Ƙasa, takardar dakatarwa daga jam’iyya.

Wannan sabuwar dakatarwar dai ta fito ne daga wani gungun da ya kira kan sa halastattun shugabannin APC na ƙauyen Ganduje, sun ce sun dakatar da Ganduje bisa dalilai na zargin sa da yi wa jam’iyyar APC zagon-ƙasa, wato ‘anti-party’.

Haka dai wani mai suna Ja’afar Ganduje wanda ya yi wa manema labarai jawabi ya bayyana a ranar Lahadi.

Ja’afar ya ce ya na magana ne da yawun sauran shugabanni 11 na APC da ke ƙauyen Ganduje.

Ya ce an zargi Abdullahi Ganduje da yin zagon-ƙasa ga APC a zaɓen da ya wuce na 2023.

Ya kuma yi zargin cewa Abdullahi Ganduje ya ƙi biyan kuɗaɗen harajin da APC Reshen Mazaɓa ke karɓa a hannun mambobin ta daga sama har ƙasa.

Ya kuma zargi Abdullahi Ganduje da haddasa husumar da ta raba kan shugabancin APC a Mazaɓar Ganduje.

People are also reading