Home Back

JADAWALIN TANTAGARYAR TA’ADDANCI: ‘Mun kai hare-hare 232 a Najeriya, farmaki 1,115 a Afrika ta Yamma a cikin watanni ukun farkon 2024’ – ISWAP

premiumtimesng.com 2024/7/24
Boko Haram Weapons
Boko Haram Weapons

Cikin wani rahoton baya-bayan nan da ƙungiyoyin ta’addanci biyu suka fitar na haɗin-gwiwa, ISWAP da ISGS sun bayyana cewa sun kai hare-haren ta’addanci sau 232 a Najeriya, a cikin watanni ukun farkon 2024, wato Janairu, Fabrairu da Maris.

Sun bayyana cewa a waɗannan hare-hare sun kashe mutum 609 a Najeriya, yayin da a Afrika ya Yamma baki ɗaya kuwa sun kai hare-hare 1,115.

ISWAP ƙungiyar Boko Haram ce wadda ta ɓalle daga biyayya ga Shekau a cikin 2016, ta riƙa kiran kan ta IS, wato Islamic State, Reshen Afrika ta Yamma.

Ƙungiyar ta Boko Haram ta yi kaka-gida ne a yankin Tafkin Chadi, ta mamayi cikin Najeriya, Kamaru da Nijar da Chadi.

Cikin wani jadawalin farfaganda da ISWAP suka fitar a ranar 1 ga Yuli, sun ce ISWAP sun kai hare-hare sau 536 wanda ya yi sanadiyyar kisan mutum 2,142.

PREMIUM TIMES ta yi nazarin jadawalin wanda ya nuna cewa ISWAP da ISGS sun kai hare-haren ta’addanci sau 1,115 a Afrika ta Yamma.

Wannan adadin ya nuna hare-hare da suka kai Afrika ta Yamma, ya ma haura rabin adadin hare-hare 2,142 da ‘yan ta’addar suka kai a Afrika baki ɗaya, a cikin watanni ukun farkon shekarar 2024.

ISWAP sun kashe mutum 609 a hare-hare 609 da suka kai Najeriya, sai kuma Kamaru da suka ka kashe mutum 40.

ISGS kuwa ta kai hare-hare 73, inda ta halaka mutum 446 yankunan ƙasar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar.

ISGS kamar yadda jadawalin ya nuna, ta kashe mutum 224 a Jamhuriyar Nijar, wasu 180 a Mali, sai kuma mutum 62 a Burkina Faso.

Can a ƙasar Kongo kuwa, ISCAP, wato ‘yan Boko Haram na Tsakiyar Afrika, sun kai hare-haren ta’addanci sau 135, suka halaka mutum 762.

Reshen IS na Zimbabwe kuwa sun ce sun kashe mutum 137 a hare-hare 68 da suka kai.

Haka nan a ƙasar Somaliya IS sun kashe mutum 128, suka kai hare-haren ta’addanci sau 14.

Kada a manta kuma akwai hare-hare na ta’addaci da ya haddasa asarar rayuka da IS ta nuna ita ce ta kai hare-haren a yankin Asiya, Turai da Gabas ta Tsakiya.

Jadawalin da IS ta fitar ya nuna cewa sun kashe mutum 500 a Rasha, wasu 393, a Siriya, sun kashe mutum 303 a Iran, Sai Pakistan inda suka kashe mutum 142, sai mutum 138 a Afghanistan, 96 a Iraqi, 33 a Philippines mutum 33, dai Turkiyya mutum biyu.

A hare-hare 788, “an kashe mutum 3,749, aka jikkata 51, cikin su har da sojojin Najeriya da kwamandojin su,” cewar rahoton ISWAP ɗin.

A cikin watanni ukun farkon shekarar 2024, “yan ta’addar sun banka wa gidaje 1,400 wuta, sun fasa kantina kamar yadda IS ta yi iƙirarin yin haka ɗin.

‘Yan ta’addar sun ce sun kai farmaki sau 47 kan coci da barikin sojoji.

Sun ce sun ƙone motoci 202, sun ƙwaci motoci 25 a matsayin ‘ganima’.

Sai kuma rahotanni sun nuna fiye da mutum miliyan 35 na neman tallafi saboda tashe-tashen hankula a yankin Tafkin Chadi, wanda ya haifar da asarar dubban rayuka.

People are also reading