Home Back

KALLO YA KOMA KANO: Kwamitin Binciken Gwamnatin Ganduje ya fara zaman haramar tone-tone da bankaɗe-bankaɗe

premiumtimesng.com 2024/5/17
Ban yi kira da a tsige ko Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC ba – Gwamna Alia

Kwamitin Binciken Gwamnatin Ganduje, wanda Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya kafa, ya fara zaman sa a Kano, a ranar Litinin.

Gwamna Abba ya kafa kwamitin domin binciken shekaru takwas na gwamnatin Abdullahi Ganduje, wanda a yanzu shi ne Shugaban APC na Ƙasa.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin Mai Shari’a Faruk Adamu, zai binciki yadda aka sayar da kadarorin gwamnati a zamanin mulkin Ganduje, sannan kuma akwai canje-canjen da ake yi wa Ganduje, matar sa Hafsat, ɗan sa Umar da wasu mutum biyar ɗin da suka haɗa da wani kamfani mai suna Lamash Properties Ltd.

A zaman kwamitin ba farko a Babbar Kotun Kano ta 3 da ke Sakateriyar Audu Baƙo, a ranar Litinin, Mai Shari’a Adamu ya yi kira ga jama’a su je su kai muhimman bayanan da za su taimaka wa kwamitin binciken wajen gudanar da aikin sa.

Sannan kuma ya yi alƙawarin yin adalci.

PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda Gwamna Abba “Ya kafa Kwamitocin Binciken Yadda aka Sayar da Kadarorin Gwamnati, Ɓacewar ‘Yan Adawa da Rigingimun Siyasa tsakanin 2015 – 2023.”

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya kafa kwamitoci biyu na binciken sayar da kadarorin gwamnatin jiha, rigingimun siyasa da kuma binciken ɓacewar wasu mutane da aka daina jin ɗuriyar su daga 2015 zuwa 2023.

Da ya ke ƙaddamar da kwamitocin a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu, Gwamna Abba ya sha alwashin sai an hukunta duk wani da aka samu da hannu wajen aikata laifi ko laifukan da za a binciko.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, Sanusi Bature ya fitar a ranar Alhamis, gwamnan ya tunatar wa kwamitin binciken salwantar Kadarorin cewa binciken wannan badaƙala na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka a ranar da aka rantsar da shi.

“Hargitsin siyasa na daga cikin abin da ke kawo koma-baya a dimokraɗiyya duk duniya. Kuma shi ne ke kai ga asarar rayuka da dukiyoyi da rashin amannar da talakawa ke yi wa masu mulki.”

“Akwai munanan rikice-rikicen da suka haifar da rasa rayuka musamman a 2023, waɗanda ba za a ba su baya a manta da su ko a binne su ba. Za a binciko su domin tabbatar da irin haka ko makamancin hakan bai sake faruwa ba.”

Kwamiti na farko ya na ƙarƙashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, shi ne kuma zai binciki rigingimun siyasa na 2015 zuwa 2023.

“Shi wannan kwamitin muna so ya binciko irin yadda aka ƙulla rikicin, sannan a bankaɗo waɗanda duk ke da hannu ko ma su wane, domin a hukunta su. Kwamitin zai bankaɗo musabbabin tashin rikice-rikicen a 2015, 2019 da 2023.”

Shi kuma kwamiti na biyu da ke ƙarƙashin Mai Shari’a Faruk Lawan, shi ne wanda Gwamna Abba ya ɗora wa nauyin bibiya da bankaɗo yadda aka sayar da kadarorin gwamnatin Kano.

Abba ya hori kwamitin da sauran ɗaukacin mambobin sa kada su saurara ko jan-ƙafa wajen gano yawan kadarorin gwamnati da aka sayar, musamman lokacin gwamnatin da ya gada.

Ya ce a gano yawan kadarorin na gwamnatin Kano da aka salwantar a ciki da wajen jihar Kano.

Sai dai Gwamna Abba ya ce wannan gagarimin aikin da ya ɗauko ba siyasa ba ce, kuma ba wasu ɗaiɗaikun mutane ya ke harin kamawa ba.

Ya ce nauyi ne da alar Jihar Kano ta ɗora masa, shi kuma zai cika alƙawarin saukewa.

Gwamnan ya ba kwamitin watanni uku ya kammala bincike tare da miƙa masa rahoton sakamakon bincike.

Binciken Ganduje: Abdul’aziz Ganduje Ya Ce Zai Taimaka Wajen Bada Bayanai, Kan Binciken Da Ake Yi Wa Gwamnatin Mahaifin Sa:

Ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje ya ce zai taimaka wajen bada bayanai kan binciken da ake yi wa mahaifin sa kan cin hanci da rashawa.

Abdulaziz ya sanar da hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga Shugaban Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji.

Idan za a iya tunawa a shekaru biyun da suka gabata, Abdulaziz ya maka Mahaifiyar sa Hafsat Ganduje a kotu.

Daga cikin abubuwan da ake binciken Ganduje dai akwai karɓar cin-hanci na Dala 413,000 da kuma sabarƙalar kuɗaɗe, ciki har da wasu Naira biliyan 1.38, waɗanda ake tuhumar Ganduje, matar sa Hafsat, ɗan sa mai suna Umar, wasu mutum huɗu da wani kamfani mai suna Lamash Properties Ltd.

People are also reading