Home Back

Gwamna Ya Lashe Amansa Kan Taimakon Masallaci, Ya Shawarci Musulmai Kan Ba da Zakka

legit.ng 2024/7/24
  • Yayin da ya sha suka kan kalamansa ga ƴan fansho, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shawarci al'ummar Musulmi kan ba da Zakka
  • Sanwo-Olu ya shawarce su da su rinƙa ba da Zakka da sadaka domin samun lada da kuma rage talauci a tsakanin al'umma
  • Gwamnan ya ce ba da Zakka da sadaka na daga cikin rukunan Musulunci wanda yake da matukar tasiri a rasuwar Musulmai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya shawarci Musulmai kan ba da Zakka.

Sanwo-Olu ya hori alummar Musulmai da su rinƙa ba da Zakka da kuma taimakon marasa karfi a yankunansu.

Gwamna ya shawarci Musulmai kan ba da Zakka
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bukaci Musulmai su ba da Zakka ga marasa karfi. Hoto: Babajide Sanwo-Olu. Asali: Getty Images

Lagos: Sanwo-Olu ya fadi amfanin Zakka

Gwamnan ya fadi haka ne yayin taron kafa Gidauniyar Zakka da wakafi a jihar, kamar yadda Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamna, Dakta Kadri Hamzat shi ya wakilci Sanwo-Olu inda ya ce hakan zai taimaka wurin dakile talauci a tsakanin al'umma.

Hamzat ya ce Zakka na daga cikin shika-shikan Musulunci wanda ya zama dole ga Musulmin da ya ke da hali, cewar Punch.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna ya sha suka kan kalamansa na taimakon masallaci da coci a wannan mako.

Sanwo-Olu ya gargadi ƴan fansho

Legit Hausa ta ruwato Sanwo-Olu yana ba ƴan fansho shawarar yadda za su kashe kudinsu da suka sha wahala yayin da suke aiki.

Gwamnan ya bukace su da kada su ba da gudunmawa a masallaci ko coci bayan wahalar da suka sha inda ya ce ya kamata su yi amfani da kudin game da matsalolinsu.

Wasu sun yaba da wannan shawara yayin da da dama suka caccake shi kan cewa ba shi zai fada musu yadda za su kashe kudinsu ba.

Ambaliyar ruwa ya yi barna a Lagos

Kun ji cewa bayan jan kunne da hukumar NIMET ta yi kan barkewar ambaliyar ruwa a Najeriya, ruwa ya mamaye jihar Lagas.

Rahotanni sun tabbatar ruwan kamar da bakin kwarya ya raba mazauna Ibeju-Lekki da muhallansu, yayin da kowa ke neman mafaka.

Asali: Legit.ng

People are also reading