Wike vs Fubara: Fusattatun Matasa Sun Fatattaki Shugaban Karamar Hukuma Daga Ofis
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Rikicin siyasa da yake faruwa tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya canza salo.
A wani sabon salo da rikicin ya dauka ya shafi shugabannin ƙananan hukumomi da gwamna Siminalayi Fubara ya umurci su sauka daga matsayinsu.
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wasu fusattatun matasa sun fatattaki shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON) na jihar yayin da ya yi yunkurin shiga ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jiya, Litinin, 17 ga watan Yuni shekarun da doka ta ba shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Ribas ya kare.
Sai dai wasu daga cikinsu sun yi alwashin cigaba da zuwa aiki karkashin wata doka da aka kirkira cewa tun da ba a yi zabe ba an ƙara musu wata shida.
Amma duka da haka Gwamna Siminalayi Fubara bai amince da ikirarin nasu ba kuma ya umurce su da su fice daga ofis.
Shugaban kungiyar ALGON ta jihar, Allwell Ihunda yana cikin masu goyon bayan Wike da suka yi alwashin cigaba da zuwa ofis.
Saboda haka a yau Talata ya kama hanyar zuwa ofis inda ya yi karo da wasu fusattatun matasa suka far masa, rahoton Vanguard.
Allwell Ihunda ya shiga mota ya ruga yayin da jami'an tsaro suka yi kokarin tare matasan daga kai masa hari.
A wani rahoton, kun ji cewa yayin murnar cika shekara daya a kan mulki, gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda aka bar masa tarin bashi.
Gwamna Fubara ya kuma bayyana dalilin da yasa tsohon gwamna Nyesom Wike ya fara yakarsa tun wata uku da zamansa gwamna a jihar.
Asali: Legit.ng