Home Back

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

leadership.ng 2024/4/27
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

A jiya ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi karatu na biyu a kan kudirin dokar tilasta wa masu niyyar yin aure yin gwajin cutar kanjamau, cutar hanta da kuma duba kwayoyin jini (sikila) kafin aure.

Musa Ali Kachako (Mazabar Takai) wanda ya kawo kudirin dokar, ya bayyana cewa, jihar na fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka hada da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba.

Ya ce, kudirin dokar idan har aka amince da shi, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaduwar cututtuka masu barazana ga rayuwa.

Aminu Sa’ad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce, jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar don kare lafiyar ‘yan jiharta ta hanyar samar da gwaje-gwaje kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka, kamar cutar hanta.

 
People are also reading