Home Back

Nijar ta kwace izinin hakar ma'adinai daga Kamfanin Orano

dw.com 2024/7/2
Niger französische Uranmine bei Arlit
Hoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

 A wata wasika ce dai da ministan kula da harkokin mu'adinai na kasar ta Nijar kwamishina kanal Abarchi Ousmane, ya aike wa babban Darektan wannan ma'aikata ta IMOURAREN SA da ke Yamai a ranar Alhamis 20 ga wannan wata na Yuni 2024, ministan ya ce dalilin wannan wasika shi ne na sake dawo da wannan hakar Uranium ta IMOURAREN ga hannun gwamnatin Nijar, inda cikin wasikar ministan ke cewa, har sau biyu mun baku takardar kashedi na cewa ku soma aikin hakar Uranium na IMOURAREN cikin watanni uku daidai da yadda ka'idojin dokoki na aikin hakar ma'adinai suka tanada kamar yadda kuma gwamnatin Nijar ba aminta da shi. Sai ga shi wannan wa'adi ya cika a ranar 19 ga watan Yuni na 2024 kuma kamar yadda na rubuta muku a ranar bakwai ga watan Yuni tsarin da kuma gabatar mana a wasikar ranar 26 ga watan Afrilu bai gamsar da mu ba don sabili da haka bisa aiki da kudiri na 59 da 61 na dokar mu'adinai ta ran biyu ga watan Maris na 1993 da ta bada wannan takardar izini wanan fili na hakar mu'adinai na IMOURAREN ya dawo ga hannun  gwamnati.

Nijar na bin kadin kafanonin hako ma'adinai na kasar

Wani bincike dai da kungiyoyin fararan hula suka yi ya nunar cewar akwai Lasisi kimanin 182 na hakar ma’adinai ko kuma na binciken ganin ko akwai ma’adinan amma ya zuwa yanzu a cewarsu ba su fice 10 da suka yi wannan aiki ba, wanda suke ganin ya kyautu a karbe duk wani wanda bai bi  ka’idojin aikin ba.

People are also reading