Gwamnati Ta Ba Masu Sana’ar PoS Sabon Umarni Yayin da Wa’adin Rijista da CAC Ya Kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Bayan karewar wa'adin watanni biyu da aka dibar masu, hukumar kula da kamfanoni (CAC) ta tsawaita wa’adin rajistar sana'a ga masu PoS zuwa ranar 5 ga Satumba.
Hukumar ta ce an tsawaita wa’adin farko na ranar 7 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Satumba; karin kwanaki 60 domin ba masu sana'ar PoS damar yin rijista.
Hukumar ta CAC ta sanar da tsawaita wa’adin ne a ranar Asabar a cikin wata sanarwa da fitar kuma aka rabawa manema labarai, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta ce matakin tsawaita wa'adin na da nufin samar da isasshen lokaci ga masu gudanar da sana'ar PoS su kammala rajistar sana'arsu.
Jaridar Tribune ta ruwaito sanarwar ta ce:
“Hukumar kula da kamfanoni tana son sanar da masu sana'ar PoS cewa an tsawaita wa’adin farko na 7 ga Yuli 2024 na rijistar sana'o'in su zuwa ranar 5 ga Satumbar 2024.
"Wannan zai baiwa masu sana'ar da ke karkara, waɗanda wataƙila suke fuskanci ƙalubalen sadarwa wajen yin rajistar damar kammala rijistar cikin sauki."
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnati ta ba kamfanonin kamfanonin da ke sarrafa na'urar PoS wa'adin watanni biyu su yi wa abokan huldarsu rijista da hukumar CAC.
Shugaban hukumar kula da kamfanoni (CAC), Hussaini Ishaq Magaji ya ce yi wa masu sana'ar PoS rijista zai kare kasuwancinsu daga 'yan zamba da kuma kutse.
Asali: Legit.ng