Home Back

Ƴan Bindigar Nijeriya Sun Kai Hari Ƙasar Niger

leadership.ng 2024/7/1
Ƴan Bindigar Nijeriya Sun Kai Hari Ƙasar Niger

Rundunar sojin Nijar ta sanar da cewa wani gungun mutane masu ɗauke da makamai daga Nijeriya ne suka far wa wata mota, inda suka hallaka mutum huɗu.

TRT Afrika ya rawaito cewa, hukumomi Nijar sun tabbatar da kashe Sojojin da da wasu jami’an Nijar a harin kwanton-ɓaunae kusa da iyakar Nijeriya.

Sojin Nijar kamar takwarorinsu na Nijeriya suna fama da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban na ƙasar.

A cewar Sojijin, “Ranar Laraba ne wani gungun masu ɗauke da makamai daga Nijeriya suka far ma wata mota, inda suka hallaka mutum huɗu”, amma hukumomin ba su fayyace waɗanda abin ya rutsa da su ba.

Sanarwar ta ce daga baya maharan sun “koma cikin Nijeriya”. Mazauna yankin sun ce waɗanda aka kashe ɗin sun je ziyara ne Diffa, wani yanki da ya sha fama da yawaitar muggan hare-haren Boko Haram da ISWAP, tun 2015.

People are also reading