Home Back

Ko Trump zai iya yin takara bayan samun sa da laifi?

bbc.com 2024/7/6
...

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Holly Honderich
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington DC

Sakamakon samunsa da laifuka 34 da aka tuhume shi da su bayan shaidu sun tabbatar da laifukan.

Kimanin kwanaki biyu ana sauraron karar, masu taimaka wa alkalai yanke hukunci 12 sun samu tsohon shugaban Amurka, Donald Trump da laifukan da suka shafi almundahanar kudi.

Shari'ar ta kasance ta tarihi, inda a yanzu Mista Trump ya kasance tsohon shugaban Amurka na farko da aka samu da aikata laifi, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar hamayya.

Yanzu me ya rage?

Ga wasu muhimman abubuwan lura.

Zai iya ci gaba da takararsa?

Kwarai kuwa! Kundin tsarin mulkin Amurka bai yi tanadin sharuda masu tsauri ba, ga masu bukatar tsayawa takarar shugaban kasa.

Sharudan su ne dole ne dan takara ya kai shekara 35, kuma ''wanda aka haifa a Amurka'' yake da takardar zama dan kasa, kuma yake zaune a kasar na akalla shekara 14.

Babu dokar da ta hana mutum tsayawa takara don an same da aikata laifi.

To sai dai hukunci ka iya dagula zaben shugaban kasa da ke tafe cikin watan Nuwamba.

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da jaridun Bloomberg da Morning Consult suka gudanar a farkon wannan shekara ya nuna cewa kashi 53 na masu zabe a manyan jihohi sun ce za su iya kin zabar jam'iyyar Republican idan aka samu Trump da laifi.

Wata kuri'ar da jami'ar Quinnipiac ta gabatar a wannan wata, ya nuna cewa kashi 6 na magoya bayan Trump, za su iya kin zabarsa, a wannan takarar da ake ganin za ta yi zafi.

Me zai faru da Trump yanzu?

Trump na karkashin beli a duka lokacin da aka kwashe ana shari'ar, kuma babu abin da zai sauya bayan samunsa da laifi a ranar Alhamis , an sake shi bisa kimar da yake da ita a kasar.

Zai koma kotun rana 11 ga watan Yuli, ranar da mai shari'a, Juan Merchan ya saka domin yanke hukunci.

Akwai abubuwa da dama da alkalin zai yi la'akari da su wajen yanke hukuncin, ciki har da shekarun Trump din.

Hukuncin zai iya hadawa da cin tara da lura da shi ko kuma yiyuwar zaman gidan yari.

Asalin hoton, Getty Images

Adult film actress Stormy Daniels (Stephanie Clifford) exits the United States District Court Southern District of New York for a hearing related to Michael Cohen, President Trump's longtime personal attorney and confidante, April 16, 2018 in New York City
Bayanan hoto, Lauyoyin Trump ka iya amfani da shaidar Stormy Daniels don daukaka kara

Trump ya bayyana hukuncin a matsayin ''abin takaici'' kuma zai daukaka kara kan lamarin, abin da kuma ka iya daukar watanni ko ma fiye.

Lauyoyinsa za su tunkari kotun daukaka kara a Manhattan.

Hakan na nufin ko da bayan yanke hukuncin, ba lallai ne Trump ya fita kotun da ankwa a hannunsa ba, saboda zai ci gaba da kasancewa a karkashin beli idan ya daukaka karar.

Kan wane dalili zai daukaka kara?

Shaidar da tauraruwar fina-finan batsa Stormy Daniels, wadda ta zargi Trump da yin lalata da ita, shi ne babban batu a shari'ar, kuma yana iya kasancewa daya daga cikn dalilan daukaka kara.

“Yadda ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ta yi zargin mu'amalar ta kasance tsakaninsu, ba lallai ne ya kasance hakan ba,'' in ji Anna Cominsky, Farfesa a fannin shari'a a jami'ar New York.

"A gefe guda kuma, yadda ta yi cikakken bayanin za ka iya gaskata ta, kuma matsayinka na mai gabatar da kara, kana bukatar gabatar wa alkali cikakkun bayan da zai yarda da kai, a daya gefen kuma akwai inda za a yi tabbata da labarin''.

Sau biyu lauyoyin Trump na sukar Ms Daniels a lokacin da take gabatar da shaidar, matakin da alkalin ya yi watsi da shi.

Bayan haka, yadda alkalin ya tafiyar da shari'ar ka iya bayar da damar daukakar karar.

Yin karya a takardun kasuwanci na iya daukar karamin hukunci, amma shi Trump yana fuskantar manyan tuhuma saboda laifinsa na biyu, wato zargin yunkurin murde zaben 2016.

Shin Trump zai je gidan yari?

Zai iya yiwuwa, to amma fa ba lallai ba ne ya yi zaman kaso.

Duka tuhuma 34 da aka yi masa, laifuka ne da ke ajin rukunin E, a birnin New York, wato laifuka mafiya kankanta a jihar. Duka laifi daya ka iya daukar hukuncin daurin shekara hudu.

Kamar yadda aka yi bayani a sama, akwai dalilan da za su sanya alkalin ya zabi yanke wa Trump hukunci mai sauki, ciki har da la'akari da shekarunsa, da kuma rashin samunsa da laifi a baya.

Haka kuma zai yi la'akari da saba wa umarnin kotu da Trump ya yi a lokacin da ake shari'ar.

Sannan akwai yiwuwar alkalin zai auna girman laifin da babu tsohon shugaban kasar da ya taba aikata shi, domin ya kauce wa daure tsohon shugaban kuma dan takara a zabe mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images

A marcher holds a sight that says "Lock Him Up!"with a picture of President Donald John Trump behind bars the Speaker of the United States House of Representatives who just submitted the articles of Impeachment for President Donald John Trump as she walks in front of Trump International Tower during the Woman's March in the borough of Manhattan in NY on January 18, 2020, USA
Bayanan hoto, Mafi yawan masu sanya idanu na ganin ba lallai ne a tura Trump gidan yari ba.

Akwai kuma masu tambayar cewa idan ma aka kai shi gidan yari, a matsayinsa na tsohon shugaban Amurka zai ci gajiyar tsaro daga jami'an da ke bai wa tsoffin shugabannin kasar kariya.

Hakan na nufin dole a ware wasu jami'an domin ba shi kariya a lokacin da yake zaman gidan yarin.

Ko ma hakan ta faru, to gudanar da gidan yarin zai zama mai wahala, kasancewar tsohon shugaban kasa ke cikinsa a matsayin fursuna.

Zai zama da cikakkiyar barazana ga tsaro, da kuma kashe makudan kudi wajen kula da gidan yarin.

“Shi gidan yarin zai lura da abu biyu: Tsaron gidan da kuma rage kudin da ake kashewa,” in ji Justin Paperny, darakta a wani kamfanin kula da gidan yari.

Kasancewar Trump a cikinsa, “zai zama wani wuri na musamman, don haka ba za a yi wasa da shi ba”, in ji shi.

Zai iya yin zabe?

Trump zai iya samun damar kada kuri'arsa a zaben.

A karkashin dokokin Florida , inda Trump ke zaune, mutumin da aka samu da babban laifi a wata jihar ba zai samu damar kada kuri'a ba, idan dai laifin zai hana shi zabe a jihar da aka same shi da aikata laifin.

Hakan na nufin matsawar Trump ba ya gidan yari ranar 5 ga watan Nuwamba, to yana da damar kada kuri'a a zaben da ke tafe.

Zai iya yafe wa kansa?

Ina! Shugaban kasa na yafe wa mutanen da suka yi wa gwamnatin tarayya laifi ne kawai.

Laifukan da suka shafi almundanar kudi a New York laifi ne da ya shafi jiha, ma'ana ba ya cikin da'irar laifukan da Trump zai yafe ko da ya sake zama shugaba kasa.

Haka batun yake a shari'ar da ake yi masa a jihar Georgia, inda ake zarginsa da laifin hada baki domin rage yawan tazarar da Biden ya ba shi a zaben 2020.

Wannan shari'a a yanzu ita ma tana matakin daukaka kara.

People are also reading