Kasuwa Ta Buɗewa Faston Dake Siyar Da Sabulu, Turare, Riga Da Masoron "Mu'ujiza"
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Legas - Jeremiah Fufeyin, faston da ya assasa cocin CMDM, ya janyo cece-kuce a soshiyal sada zumunta bayan da ya ƙaddamar da wani sabon salon kasuwanci tare da ci da addini.
Soshiyal midiya dai ta rikice da bidiyon Fasto Fufeyin yana nuna sabulu, turare, riga da masoro da ya yi ikirarin na mu'ujiza ne.
A wani bidiyon zaman addu'a na kai tsaye da aka wallafa a shafin Facebook, an fa Fasto Fufeyin da matarsa, Anthonia, sun kaddamar da kayayyakin da suka ce na mu'ujiza ne.
Faston ya ce sabulun yana da ƙarfi kuma zai iya magance kowacce cuta, inda yace sabulun zai taimakawa mutanen da ke da rashin sa'a ko samun tsaiko a cimma burikansu a rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta ruwaito Fasto Fufeyin ya bayyana cewa wasu mutane na fama yayin da wasu ke halartar cocinsa ba tare da sani koyarwa Ubangiji ba.
Yayin wa'azin na kai-tsaye, Fasto Fufeyin ya yi ikirarin cewa turaren da ya sarrafashi yana karya duk wani shingen rashin nasara ta dan Adam.
"Akwai wasu mutane wadanda duk abin da za su yi basa samun ci gaba, hatta kudin da ke asusun bankinsu ba sa karuwa sai dai su ragu.
"Irin waɗannan mutanen na buƙatar amfani da irin wannan turare. Wannan turaren yana ba da gudumawa wurin samun nasara.
- A cewar malamdin addinin.
Kamar yadda malamin addinin ya bayyana, masoron da ya sarrafa na iya sa a tsallake duk wata matsalar da wanda ya sayi fili amma ya kasa ginawa yake fuskanta.
Hakazalika ya bayyana wata riga wacce yayi iƙirarin cewa tana bada kariya sannan tana kawo albarka.
Kalli bidiyon a kasa:
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa ministan babban birnin tarayya, ya rikita 'yan Najeriya da salon gayunsa da aji a Abuja.
An ga wani bidiyo wanda ya nuna Wike ya saka rigar kusan Naira miliyan uku inda ya halarci wani taro, lamarin da ya haifar da cece kuce a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng