Home Back

Kotu Ta Rushe Dokar Da Ta Tsige Aminu Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano

leadership.ng 2024/6/29
Makomar Masarautun Kano Ta Fara Tayar Da Kura A Jihar

Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano, ta yi watsi da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke dokar masarautar Kano.

Majalisar dokokin Kano ta soke dokar da ta samar da masarautu biyar a jihar, inda daga baya Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar da majalisar ta zartar tare da tsige, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

Gwamnan ya rushe masarautu biyar da suka hada da Bichi da Rano Karaye da kuma Gaya da magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Bayan tsige sarakunan, gwamnatin jihar ta dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda Ganduje ya tsige a shekarar 2020, a matsayin Sarkin Kano na 16.

Sai dai, Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba, ya kalubalanci yadda aka aiwatar da dokar, inda ya bukaci kotun ta bakin lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ta soke dokar.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis,  Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya yi watsi da matakin da gwamnatin Kano ta dauka, inda ya umarci masarautun su ci gaba da zama daram.

People are also reading