Home Back

Darajar naira: Yaushe ‘yan Najeriya za su gani a ƙasa?

bbc.com 2024/5/10
Naira da dala

Asalin hoton, getty images

Wani rahoto da jaridar Bloomberg da ke Birtaniya ta fitar ya bayyana takardar kuɗin Najeriya wato naira a zaman ɗaya daga cikin waɗanda darajarsu ta fi ɗaukaka a duniya yanzu haka.

A cewar rahoton, darajar nairar ta karu tun watan Maris ɗin wannan shekarar kawai.

Masana tattalin arziki sun ce hakan na da nasaba da matakan farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da Babban bankin ƙasar CBN da kamfanin mai na NNPCL suka ɗauka.

Alhaji Shu'aibu Idris Mikati, masanin tattalin arziki ne a Najeriya kuma ya shaida wa BBC cewa ba wani abin mamaki ba ne saboda gwamnatin ƙasar da kuma babban bankin Najeriya sun ɗauki matakan da ya kamata.

"Na farko dai, an samu an biya basussukan da ake bin babban bankin Najeriya musamman kamfanonin jiragen sama waɗanda suka haɗa kuɗaɗe sama da dala miliyan 500 zuwa biliyan ɗaya, an samu an biya.

"Babban bankin Najeriya ya ƙafe da ƙarfi da ƙatafaren kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC inda aka ciyo bashin dala biliyan 3.7 daga wani bankin da ke ƙasar Masar da ake kira da 'Afrexim Bank'." In ji masanin.

Mikati ya ce waɗannan basussukan da wannan bankin na Masar ya bayar ya taimaka wajen ƙara ƙarfin darajar naira.

Masanin tattalin arziƙin ya kara da cewa akwai basussuka ƙanana-ƙanana da ake bin Babban bankin Najeriya amma kuma Babban bankin ya samu ya biya.

"Duk lokacin da aka ce da ana bin ka bashi kuma ka samu ka biya, za ka ga cewa ka ɗan samu damar da za ka yi walwala." in ji masanin tattalin arziƙin.

Ana biyan bashi da kuɗin bashi?

Miƙati ya ce ba kuskure ba ne a nau'i na jari hujja idan aka ce za a biya bashi da kudin bashi.

Masanin tattalin arziƙin ya ƙara da cewa za a iya ƙarɓar sabon bashin da za a bai wa mutum damar biya bayan wani dogon lokaci domin ya biya bashin da ya kamata ya biya a ƙanƙanin lokaci.

"Idan ana bi na bashi wanda ya kamata na biya nan da sati guda, ko biyu ko kuma wata ɗaya, kuma na sami wani sabon bashi da za a ba ni dama in biya nan da shekaru biyar, ba kuskure ba ne in ɗauki bashin domin na biya bashin da ake bi na wanda ya kamata in biya nan da wata ɗaya". in ji shi.

Yaushe 'yan Najeriya za su gani a ƙasa?

Masanin tattalin arziƙin ya ce amfanin farfarɗowar da darajar naira ke yi na nan tafe inda ya ce a wasu wurare an fara samun amfanin farfaɗowar darajar nairar.

"Yanzu kamar tikitin da ake siya na zuwa ƙasashen ƙetare, za a ga cewa kashi 25 cikin 100 na farashin da ake siyarwa kamar watanni biyu ko uku da suka wuce, an rage.

Ashe ko an fara samun amfanin tagomashin da nairar ta samu." Mikati ya ce.

Ya ƙara da cewa kayan da ake saye a canjin yanzu ba su riga sun fara shiga kasuwanni ba yayin da kuma kayan da ake da su a kasuwannin har yanzu waɗanda aka riga aka siya ne a lokacin da dala take da tsada shi ya sa kayayyaki ke tsada har yanzu duk da tagomashin da naira ta samu.

People are also reading