Home Back

Hukumar NEMA Ta Raba Kayan Abincin Da Kungiyar Bada Agaji Ta Saudiyya Ta Bayar Ga Gidaje 2,056 A Kano

leadership.ng 2024/5/13
Hukumar NEMA Ta Raba Kayan Abincin Da Kungiyar Bada Agaji Ta Saudiyya Ta Bayar Ga Gidaje 2,056 A Kano

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), a ranar Talata, ta fara rabon kayan abinci da cibiyar agajin jin kai ta Sarki Salman (KSrelief) ta bayar ga iyalai 2,056 a jihar Kano.

Shugabar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, a lokacin da take kaddamar da rabon kayayyakin a Kano, ta ce, an yi hakan ne domin tallafa wa marasa karfi, da kuma dakile tsadar rayuwa.

NAN ta rahoto cewa, kungiyar KSrelief na bayar da agajin jin kai ga mabukata a wajen iyakokin masarautar.

Shugabar Hukumar ta NEMA, wacce Darakta ce a bangaren ayyuka na musamman ta wakilta, Hajiya Fatima Kassim, ta ce, tallafin abincin ya zo kan lokaci, domin ya zo daidai da watan Ramadan.

Ta ce “kowane gida zai samu kayan abinci, da suka hada da shinkafa (25kg), wake (25kg), masa vita flour (4kg), tumatur (2kg), man gyada (lita 2), maggi (0.8kg) da gishiri 1kg.

People are also reading