Home Back

ASUU Ta Bayyana Matsayarta Kan Shiga Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago

legit.ng 2024/7/3

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci ɗaukacin mambobinta na ƙasa baki ɗaya da su shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara.

ASUU ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin tare da sauran ma'aikatan Najeriya a ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.

ASUU ta shiga yajin aiki
ASUU ta umarci mambobinta su shiga yajin aikin NLC da TUC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Twitter

Ƙungiyar ta kuma umurci shugabannin rassanta na jami’o’i daban-daban da su haɗa kan ƴan ƙungiyar da ke ƙarƙashinsu domin bin umarnin shiga yajin aikin, cewar rahoton jaridar Tribune.

Ƙungiyar ASUU ta bayar da wannan umarni ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Yunin 2024, mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa Farfesa Emmanuel Osodeke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar an aika da ita ga dukkan shugabannin rassan ƙungiyar na jami'o'i da jagororin ƙungiyar na shiyya-shiyya.

"NLC ta sanar da fara yajin aiki daga ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024 sakamakon gazawar gwamnati wajen kammala tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi da janye cire tallafin wutar lantarki."
"Ana umartar rassanmu da su shiga yajin aikin a matsayinmu na ƙungiyar da ke da alaƙa da ƙungiyar ƙwadago."

- Farfesa Emmanuel Osodeke.

Asali: Legit.ng

People are also reading