Home Back

Me umarnin ICC na kama Netanyahu da shugabannin Hamas ke nufi?

bbc.com 2024/6/26
Karim Khan

Asalin hoton, Reuters

Benjamin Netanyahu ya mayar da martani a fusace game da labarin cewa za a iya bayar da izinin kama shi kan zargin aikata laifukan yaƙi da take hakkin bil'adama.

Wannan "babban rashin hankali ne a tarihi," in ji shi. Isra'ila "ta ƙaddamar da yaƙi ne a kan Hamas, ƙungiyar kisan kiyashi wadda ta kai hari mafi muni kan Yahudawa tun bayan kisan kiyashin Holocaust."

A wani mummunan suka da ya yi wa babban mai gabatar da ƙara na Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), Karim Khan - Netanyahu ya bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin "manyan maƙiya Yahudawa na wannan zamani."

Ya ce Mista Khan ya zamo tamkar daya daga cikin alƙalan zamanin ƴan Nazi a Jamus waɗanda suka hana wa Yahudawa haƙƙoƙinsu, tare da taimakawa wajen aiwatar da kisan kiyashi a kan su.

Matakin da ya ɗauka na neman a bayar da izinin kama firaministan Isra'ila da ministan tsaro "zuba fetur ne a cikin wutar ƙyamar Yahudawa da ake fama da ita a faɗin duniya."

Netanyahu ya yi magana ne cikin yaren Ingilishi a wani bidiyo da ofishinsa ya fitar. Yakan yi hakan ne idan yana son saƙonsa ya isa sosai zuwa ga al'ummar duniya, musamman Amurkawa.

Asalin hoton, LIGHTROCKET VIA GETTY IMAGES

Ana kyautata zaton cewa shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar na ɓoye a yankin na Falasɗinawa
Bayanan hoto, Ana kyautata zaton cewa shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar na ɓoye a yankin na Falasɗinawa

Lokacin da yake mayar da nasa martanin, ministan tsaro na Isra'ila, Yoav Gallant a ranar Talata ya bayyana batun kama shi da firaministan Benjamin Netanyahu a matsayin "abin kunya" kuma wani yunƙuri na tsoma baki a cikin yaƙi.

"Ƙoƙarin da mai gabatar da ƙara na kotun manyan laifuka na duniya Karim Khan ke yi na warware ƙirƙirar ba zai yi nasara ba - kwatanta ƙungiyar ta'addanci ta Hamas da ƙasar Isra'ila da mai gabatar da ƙara na kotun ya yi mummunan abu ne kuma abin ƙyama." kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Ya kuma ƙara da cewa: "Ƙasar Isra'ila ba ta cikin ƙasashen da suka amince da ikon kotun ta ICC."

Wannan ɓacin rai da firaministan da sauran ƴan siyasar Isra'ila suka nuna, martani ne kan kalaman Mr Khan, wanda shi ne babban mai gabatar da ƙara a kotun ICC kuma ƙwararren masanin shari'a a Birtaniya.

Kalaman nasa idan aka haɗa su tare da yin kyakkywanan nazari za a ga cewa sun fito da munanan zarge-zarge kan manyan shugabannin Hamas da firaiministan Isra'ila da ministan tsaro na ƙasar.

Bayanin na Mistan Khan ya fito ƙarara da aniyarsa ta ganin an yi amfani da dokokin ƙasashen duniya kan yaƙe-yaƙe a kan ɓangarorin biyu domin ganin an fitar da takardar umurnin kama waɗanda abin ya shafa.

"Babu wani ɗan saƙo ko kwamanda ko jagora na fararen hula - ko ma wane ne da zai aikata assha." Ya ce a riƙa son rai wajen aiwatar da doka ba. Idan aka yi haka, "za mu samar da yanayin lalacewar ta".

Batun tuhumar ɓangarorin biyu ta hanyar amfani da dokokin duniya ne ke janyo fushi, ba a Isra'ila kaɗai ba.

Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya ce abin "ya zarce batun hankali" a ce ana neman bayar da takardar kame.

Ya ce "babu kamanceceniya tsakanin Isra'ila da Hamas".

Hamas ta buƙaci a janye zarge-zargen da ake yi wa shugabanninta, tana zargin cewa mai gabatar da ƙarar na kotun ICC ya "yi wa wanda aka cuta ne da wanda ya yi cuta ne kudin goro".

Ta ce an yi jinkiri sosai wajen buƙatar a kama shugabannin Isra'ila, domin ya kamata a yi hakan ne tun watanni bakwai da suka wuce, bayan da "masu mamaye na Isra'ila suka aiwatar da munanan laifukan".

Mista Khan bai kamanta ɓangarorin biyu ba kai tsaye, sai dai kawai inda ya fayyace iƙirarinsa kan cewa dukkanin ɓangarorin biyu sun aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama.

Kotun ta ICC na ɗaukar yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa kasancewar tana da matsayi na mai sanya ido a Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke nufin tana da matsayin sanya hannu kan yarjejeniyar 'Rome Statute' wadda ta kafa kotun.

Mista Netanyahu ya bayyana cewa Falasɗinawa ba za su taɓa samun ƴancin kai ba a lokacin mulkinsa.

A maimakon kallon kwatanta Isra'ila da Hamas a matsayin abin kunya, kamar yadda shugaban ƙasar Isra'ila Isaac Herzog ya bayyana, "waɗannan munanan ƴan ta'adda da zaɓaɓaɓiyar gwamnatin Isra'ila", ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yaba da yadda mai gabatar da ƙarar na ICC ya buƙaci a aiwatar da doka kan ɓangarorin biyu.

B'Tselem, wata ƙungiyar kare hakkin bila'adama ta Isra'ila ta ce sammacen kamen ya kai Isra'ila matakin "lalacewar suna cikin hanzari".

Ta ƙara da cewa: "Duniya na nuna wa Isra'ila cewa ba za ta ci gaba da aiwatar da tsarinta na rikice-rikice da kashe-kashe ba tare da an tuhume ta ba".

Tsawon shekaru da dama masu rajin kare hakkin bila'adama na kokawa kan cewa manyan ƙasashen duniya bisa jagorancin Amurka na rufe idanuwansu kan yadda Isra'ila ke karya dokokin duniya yayin da suke sukar wasu ƙasashen tare da ƙaƙaba musu takunkumi.

Suna ganin cewa matakin da Mista Khan ya ɗauka abu ne da ya kamata a ce ya faru tun tuni.

Mista Khan ya ce shugabannin Hamas uku sun aikata laifukan yaƙi waɗanda suka haɗa da kisa da garkuwa da mutane da fyaɗe da azabtarwa.

Mutanen da aka ambaci sunansu su ne Yahya Sinwar wanda shi ne shugaban Hams a Gaza, Mohammed Deif, kwamandan ɓangaren sojojin Hamas na Qassam Brigades da Isma'il Haniyeh, shugaban sashen sisaysa na Hamas.

A wani ɓangare na binciken da suka gudanar, Karim Khan da tawagarsa sun tattauna da mutnanen da suka tsira daga harin 7 ga watan Oktoba.

Ya bayyana cewa Hamas ta take hakkin bil'adama.

A ɓangare ɗaya Mista Khan ya bayyana cewa Isra'ila na da damar kare kanta. Amma 'miyagun laifuka’ "ba za su zama hujja ga Isra'ila na gaza yin biyayya ga dokokin jin ƙai na duniya ba".

Gazawar hakan, in ji shi, ya cancanci a bayar da sammacin kama Mista Netanyahu da ministan tsaro Yoav Gallant kan laifukan da suka shafi hana fararen hula samun abinci a matsayin wani makamin yaƙi, kisan gilla, kisan ƙare dangi da kuma kai farmaki kan fararen hula.

Tun daga farkon martanin da Isra'ila ta mayar a kan harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba, Shugaba Biden ya sha yin hannunka mai sanda ga Isra'ila, yana nuna damuwa kan cewa tana kashe fararen hula masu yawa tare da lalata gine-ginen fararen hula da yawa a Gaza.

To amma a wani ƙoƙari na ganin bai saɓa wa ƙawar ta Amurka ba, wadda a kodayaushe suke tallafa mawa, gwamnatin Mista Biden ba ta bayyana a fili abin da take nufi ba.

Mista Khan ya bayyana abin da yake nufi ƙarara. Cewa Isra'ila ta bi hanyoyi marasa kyau wajen cimma burukanta na yaƙi - "kamar haifar da mace-mace da gangan, jefa mutane cikin yunwa, azabtarwa da raunata fararen hula".

A yanzu tawagar alƙalai na kotun hukunta manyan laifuka za su zauna domin tantance ko ya kamata a bayar da sammacen.

Idan hakan ta faru za a buƙaci ƙasashen da suka sa hannu kan dokar kafa kotun su kama waɗanda ake zargin da zarar suka samu damar hakan.

Ƙasashen 124 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kafa kotun ba su ƙunshi Rasha da China da kuma Amurka ba. Haka nan ma Isra'ila ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba.

Sai dai kotun ta bayyana cewa tana da hurumin gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata miyagun laifuka a yaƙin kasancewar yankin Falasɗinawa ya sanya hannu kan yarjejeniyar.

Idan har aka gabatar da sammacen kamen, hakan na nufin Mista Netanyahu, wanda shi ne firaiminista da ya fi daɗewa kan mulkin Isra'ila ba zai iya kai ziyara zuwa ƙasashen yamma ƙawayenta ba kasancewar zai shiga haɗarin kamawa.

Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya ce matakin kotun ta ICC "ba zai taimaka wajen dakatar da yaƙin ko kuɓutar da mutanen da ake garkuwa da su ko shigar da kayan agaji ba".

To amma idan aka bayar da sammacin kamen ya zama wajibi ga Birtaniya ta kama Netanyahu idan ya shiga ƙasar, sai dai idan ta iya bayar da hujjoji masu ƙwari kan cewa Mista Netanyahu na da rigar kariya ta diflomasiyya.

Wani sassauci ga Mista Netanyahu da Mista Gallant shi ne Amurka. Amurka na ganin cewa kotun ICC ba ta da hurumin tsoma baki a yaƙin, wani abu da zai iya ƙara rarrabuwar kawuna da ke tsakanin ƴaƴan jam'iyyar Democrats game da yaƙin.

Wasu sun riga sun yi maraba da matakin kotun ta ICC. Sai dai manyan masu nuna goyon baya ga Isra'ila na iya goyon bayan matakin da ƴan Repuiblican ke shirin ɗauka na amincewa da wata doka da za ta hana jami'an kotun ICC shiga Amurka.

Yayin da ake ci gaba da yaɗa yuwuwar cewa za a samu Isra'ila da laifi a shari’ar, wasu gungun ƴaƴan jam'iyyar Republican sun yi wata barazana ga Mista Khan, wadda wataƙila a wasannin fim kawai ya taɓa ji.

Wato "Idan ka hari Isra'ila za mu kai maka hari... muna gargaɗin ka."

Shi ma Yoav Gallant ba zai samu damar tafiye-tafiye cikin ƴanci ba. Kalaman da ya yi amfani da su wajen bayyana cewa Isra'ila za ta mamaye Gaza na cikin abubuwan da masu sukar Isra'ila ke tunowa a kodayaushe.

Kwana biyu bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, Mista Gallant ya ce: "Na bayar da umarnin mamaye ɗaukacin Zirin Gaza. Ba za su samu lantarki ba, babu abinci, babu man fetur, za a rufe komai...muna yaƙi ne da dabbobin mutane kuma muna musu abin da ya cancance su".

A cikin sanarwar da ya fitar, Mista Khan ya rubuta cewa "Isra'ila ta hana wa fararen hular Gaza samun abubuwan da suke buƙata na rayuwa".

A cewar sa bala'in yunwa ya faɗa wa wasu yankunan Gaza sannan babu makawa zai faɗa a wasu yankunan.

Isra'ila ta musanta cewa akwai bala'in yunwa, ta yi iƙirarin cewa ba hare-harenta ne suka haifar da ƙarancin abincin da ake fama da shi ba - sai dai sace-sacen abinci da Hamas ke yi da kuma rashin ƙwarewa na Majalisar Dinkin Duniya.

Idan aka bayar da sammacin kama Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren mulki na Hamas, dole ya yi taka tsantsan da irin tafiye-tafiyen da yake yi domin haɗuwa da shugabannin ƙasashen Larabawa. Da alama zai fi zama ne a matsuguninsa da ke Qatar, wadda kamar Isra'ila, ita ma ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar kotun ICC ba.

Sauran shugabannin Hamas biyu da ake zargi, wato Yahya Sinwar da Mohammed Deif, ana kyautata zaton cewa suna ɓoye ne a wani yanki na Gaza. Bayar da sammacen kama su ba zai ƙara wani matsi a kansu ba.

Isra'ila na ci gaba da ƙoƙarin kashe su tun watanni bakwai da suka gabata.

Bayar da sammacen kamen zai saka Mista Netanyahu cikin jerin shugabanni irin su shugaban Rasha Vladimir Putin da marigayi Muammar Gaddafi na Libya.

Mista Putin na fuskantar kame sanadiyyar zargin shi da kamawa da mayar da yara ƴan ƙasar Ukraine zuwa Rasha ba bisa ƙa'ida ba.

Kafin rasuwarsa, sammacin kamen da aka yi wa Kanar Gaddafi ya faru ne bisa zargin shi da kisa da tozarta fararen hula.

Wannan ƙungiya ba abu ne mai kyau ba ga Benjamin Netanyahu, jagoran ƙasar da ke bugun ƙirjin cewa tana a bisa turba ta demokuraɗiyya.

People are also reading