Home Back

Yayin da Ake Jita Jitar Sauya Shi, Ganduje Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Yi da Kowa Ya Gaza

legit.ng 2024/6/26
  • Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan irin tsare-tsaren da ya ke kawowa
  • Ganduje ya ce dukkan wadannan matakai na Tinubu suna da amfani kuma nan kusa za a fara cin moriyarsu
  • Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakwancin kungiyar shugabannin kananan hukumomi a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya ce tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu za su inganta Najeriya.

Ganduje ya ce a yanzu jam’iyyar APC ta fi kowace samun yawan jihohi da kananan hukumomi saboda kyawawan tsare-tsarenta.

Ganduje ya yabawa tsare-tsaren Tinubu a Najeriya
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya koda Shugaba Bola Tinubu kan tsare-tsarensa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu. Asali: Facebook

Ganduje ya koɗa Tinubu kan tsare-tsarensa

Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne a yau Juma’a 17 ga watan Mayu a Abuja yayin tarbar kungiyar shugabannin kananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yabawa irin kokarin shugabannin kananan hukumomin inda ya ce sune kashin bayan APC saboda kusancinsu da mutane, TheCable ta tattaro.

“Mun san irin wahalar da kuke sha daga magoya bayan APC musamman lokacin zabe da kuma na fidda gwani.
"Muna sane da irin wahalar da ke ciki, mun dauke ku kamar sojojinmu ne, muna godiya matuka da gudunmawar da kuke bayarwa."

- Abdullahi Ganduje

Ganduje ya ce Tinubu jarumi ne

Ganduje ya ce Tinubu yana da kwarewar siyasa tun daga tushe kuma zai inganta Najeriya, cewar PM News.

"Mutum ne jajirtacce kuma jarumi wanda ya dauki wasu matakai masu tsauri da sauran gwamnatocin baya suka gaza dauka."
"Nan ba da jimawa zaku fara ganin amfanin matakan da ya ke dauka, matatun mai za su fara samar da mai wadatacce a kasar."

- Abdullahi Ganduje

An sauya kotun da ake shari'ar Ganduje

Kun ji cewa Shugabar alkalan Kano, Dije Aboki ta sauya kotun da ake shari'ar shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje.

Hakan bai rasa nasaba da ci gaba da tuhumar da ake yi wa Ganduje musamman a jihar Kano kan zargin badakalar kudi.

Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar cewa an fara neman wanda zai maye gurbin Ganduje saboda matsalolin da ya ke ciki.

Asali: Legit.ng

People are also reading