Home Back

Sojoji Sun Sheke 'Yan Ta'adda 7 a Wani Sabon Artabu a Sokoto

legit.ng 2024/5/9
  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile wani yunƙurin kai harin ta'addanci da ƴan ta'adda suka yi a jihar Sokoto
  • Sojojin tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun sheƙe ƴan ta'adda bakwai a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa a jihar
  • Bayan tura ƴan ta'addan zuwa barzahu, jami'an tsaron sun kuma ƙwato bindigu da adduna a hannun miyagun masu tada ƙayar bayan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan ta'adda bakwai a jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Modachi na ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Sokoto Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne lokacin da suka daƙile wani yunkurin kai hari da suka yi bayan sun samu kiran gaggawa.

Sanarwar ta jaddada cewa, sojojin a wani samame na haɗin gwiwa sun kashe bakwai daga cikin ƴan ta'addan tare da kwato manyan makamai daga ƴan ta'addan da aka kashe.

Jami’an tsaron Najeriya sun yi artabu da ƴan ta’addan da ke kan hanyar wucewa kan babura da dama inda suka yi nasarar tura guda bakwai daga cikinsu zuwa barzahu.

Rundunar ta bayyana cewa sojojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, babura huɗu, wayoyin hannu guda biyu da adduna huɗu daga hannun ƴan ta’addan.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na runduna ta 6 da ake kira 'Whirl stroke' sun kashe ƴan ta'adda biyu a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne yayin da suka dakile wani hari a ƙauyen Kweserti da ke a ƙaramar hukumar Ussa ta jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading