Basaraken Arewa Ya Sha da Ƙyar a Hannun ’Yan Bindiga, ’Yan Sanda Sun Kai Masa Ɗauki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Wani basaraken Arewacin Najeriya ya sha da ƙyar a lokacin da wasu gungun 'yan bindiga suka kai masa farmaki da nufin sace shi.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa ta daƙile harin da 'yan bindigar suka kai wa Sarkin Ninzo, Alhaji Umar Musa.
Masarautar Ninzo na a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna, kuma an kai harin ne a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa har yanzu ba a san inda mai ɗakin basaraken take ba.
Mansir ya ce tuni aka tura jami'an tsaro zuwa dazuzzukan da ke yankin Sanga domin nemo uwar gidan basaraken.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kungiyar raya yankin Ninzo ta yi Allah wadai da wannan hari da 'yan bindigar suka kai na yin garkuwa da Alhaji Umar Musa.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Moses Audi da sakataren kungiyar, Silas Anche suka fitar, sun roki jami'an tsaro su ceto mai dakin basaraken.
Kungiyar ta kuma roki al'ummar masarautar Ninzo da su kwantar da hankula tare da ba jami'an tsaro hadin kai yayin gudanar da binciken su.
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani lauya mai kare hakkin dan Adam, Mike Ozekhome ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta ba Nasiru El-Rufai damar kare kansa.
Majalisar jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamnan da karkatar da N423bn da cin zarafin ofis, inda ta nemi a tuhumi shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Asali: Legit.ng