Home Back

Kano: Hukumar Yaki da Rashawa ta Fara Binciken Zargin Almundahana a Tallafin Gwamnati

legit.ng 2024/7/1
  • Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa a Kano ta fara binciken zargin almundahana kan tallafin da gwamnatin jihar ta raba ga masu kananan sana'o'i
  • A makon da ya gabata ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta raba tallafin N50,000 ga masu kananan sana'o'i a kan titunan jihar da zummar bunkasa tattalin arzikinsu
  • Amma a wani bidiyo, an gano yadda wasu 'jami'ai' su ka karbe N45,000 su ka bar wadanda su ka samu tallafin da N5,000 lamarin da Muhyi ya ce ba za su lamunta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Hukumar karbar korafe-korafe yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kaddamar da bincike kan wata badakala da ta shafi tallafawa masu kananan sana’o’i a kan tituna.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Kano ta kaddamar da ta tallafawa masu sana’o’in su 465 da kudi N50,000 kowannensu.

Daily Trust ta wallafa cewa an gano wani bidiyo ya nuna wasu mutane na karbar wani kaso na kudin tallafin

Ana zargin raba masu sharar da N45,000

Wani bincike ya nuna cewa wadanda babu sunayensu cikin wadanda za a bawa tallafi ne suka karbi kudin a madadinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani a ka basu N5000 daga cikin tallafin, N45,000 da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta raba musu, kamar yadda Solacebase ta wallafa.

Wani Malam Nura Isa ya bayyana cewa jami'an sun tirsasa masu rabuwa kudin ta dole. Amma shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhyi Magaji Rimingado, ya ce ba za su kyale duk wanda aka samu da hannu a ciki ba, inda ya ce a yanzu haka sun kaddamar da bincike kan batun.

Gwamnan Kano ya tallafawa talakawa

A baya kun ji labarin yadda gwamnatin jihar Kano ta tallafawa talakawa da ke kananan sana'o'i a kan tituna jihar kimanin 465.

Mai magana da yawun gwamnan jihar , Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar, inda ya ce an yi haka ne domin bunkasa tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

People are also reading