Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Batun Taso Ganduje a Gaba Sai Ya Yi Murabus
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Makurdi, jihar Benuwai - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi kira ga Alhaji Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Maris a Makurdi, babban birnin jihar ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Tersoo Kula.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa sakataran na mayar da martani ne kan rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yaɗa cewa gwamnan ya buƙaci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tersoo Kula ya ce babu wani lokaci da gwamnan ya taɓa neman shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yi murabus.
Ya ƙara da cewa Gwamna Alia yana da kyakkyawar alaƙa da shugabannin APC ƙarƙashin jagorancin Ganduje.
A kalamansa:
"Ya zama wajibi a fayyace cewa ko kaɗan Gwamna Alia bai taɓa shirya, halarta, ya aika da wakili ko shiga duk wani taro domin tattauna batun tsige ko kiran murabus ɗin Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ba."
Ya ce gwamnan ya mayar da hankali ne wajen ganin an samu canji mai kyau a jihar Benuwai, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.
Kula ya ƙara da cewa:
"Yana nan a tsaye bisa nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC a jihar Benuwai kuma yana yin duk abin da ya dace domin shirya samun nasarar jam’iyyar a nan gaba."
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam'iyyar za ta karɓe mulkin jihar Anambra daga hannun jam'iyyar APGA.
Ganduje ya yi nuni da cewa APGA ta kasa samar da ci gaban da ake buƙata a jihar wanda hakan ya sa take tafiyar hawainiya.
Asali: Legit.ng