Home Back

Doka za ta yi aiki akan duk masu tayar da hankalin al’umma yayin bikin Sallah – Ƴan Sandan Kano.

dalafmkano.com 2024/5/17

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ba za ta saurarawa ɓata garin da suka ce ba za’a zauna lafiya ba, a yayin bikin ƙaramar Sallah.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakiliyar mu A’isha Shehu Kabara, ya ce duk wasu gungun mutane da suka ce zasu ɗaukko muggan makamai da zummar tayar da hankalin al’umma ko kuma illata mutane lashakka doka za tayi aiki a kan su.

“Duk wanda ya ce ba za’a zauna lafiya ba a yayin bikin ƙaramar Sallar mu kan mu ba zamu bar shi ya nutsu ba, za muyi duk abinda ya kamata na ganin cewa an kare irin waɗannan abubuwa, “in ji SP Kiyawa”.

Ya ƙara da cewa yanzu haka Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya riga ya bada umarnin baza jami’an tsaron ƴan sandan su, kuma ciki har da na farin kaya da kuma wadata su da kayan aiki, domin yin dukkan abinda ya kamata wajen ganin an tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Rundunar ƴan sandan Kano, ta kuma shawarci masu ababen hawa da su kula yayin tuƙi a kan hanya da cikin unguwanni a yayin bikin ƙaramar Sallah, tare da kaucewa gudun ganganci, domin kaucewa afkuwar haɗura.

“Iyaye ku kula da ƴaƴan ku a yayin bikin sallar domin gujewa ɓatan su ko kuma faɗawa komar ɓata gari, a cewar sa”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake sa ran gudanar da bikin ƙaramar Sallah, a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu na shekarar 2024.

People are also reading