Kano: Har Yanzu Ganduje Bai Tsira Ba, Abba Ya Taso Shi Gaba a Wata Sabuwar Badakala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka tafiyar da biyan giratuti a baya.
Gwamnan ya sha alwashin bankado badakalar da aka yi a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje.
Abba ya zargi Ganduje da zaftare wasu kudade na giratuti a jihar ba tare da mayar da su asusun gwamnati ba, kamar yadda Channels TV ta wallafa faifan bidiyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka kan yadda babu wani shaida da zai tabbatar da ƴan fansho na bin gwamnatin bashi saboda rashin shaida da takardu na kuɗin da aka zaftare.
"Mun rasa ya za mu yi, ba za mu iya gano kudin fansho da gwamnatin da ta shude da cire ba a jihar."
"Mun yi dukkan kokari domin gano kudin inda muka tabbatar an cire su amma babu duriyarsu, ku yi duk mai yiwuwa domin nemo inda kudinku suka shiga."
- Abba Kabir
Gwamna Abba daga bisani ya shawarci kungiyar ƴan fansho da ta rubuta korafi ga gwamnatin jihar domin neman inda kudin suke.
Abba ya ce gwamnatin jihar za ta yi iya bakin kokarinta wurin binciko inda kuɗin suka maƙale tare da biyansu hakkinsu.
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗin giratuti N5bn daga shekarar 2016 zuwa 2019.
A kashi na farko, Gwamnan ya fitar da N6bn domin biyan kuɗin giratuti da waɗanda suka rasu mutum 5,333 wanda ya sanya suka kai N11bn.
Asali: Legit.ng