EFCC Ta Cafke Ministan Buhari Bisa Zargin Almundahanar Biliyoyin Kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.
Hukumar na zarginsa ne da hannu cikin bincike da ta ke a kan almundahanar kudi da ya haura naira biliyan 8.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hadi Sirika ya isa ofishin EFCC da ke Abuja ne yau Talata da misalin karfe 1.00 na rana domin gudanar da bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana bincikensa ne a kan wata kwangila da ya bawa kamfanin dan uwansa mai suna Engirious Nigeria Limited wanda mallakin kaninsa ne.
Jami'a hukumar da ba sa so a bayyana sunan su sun tabbatar da cewa hukumar ta kama tsohon ministan a yau
Kuma sun tabbatar da cewa an kama shi ne bisa zarginsa da hada kai da dan uwansa wurin karkatar da makudan kudade sama da biliyan 8, cewar jaridar Leadership
Tin a watan Fabrairu dai aka ruwaito cewa hukumar ta EFCC ta fara binciken ofishinsa bisa baba-kere da dukiyar al'umma.
Hadi Sirika yana cikin ministotin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da hukumar EFCC ke nuna wa yatsa bisa zargin karkatar da kudade.
A wani rahoton kuma, kun ji cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon ministan sufurin jiragen sama
An tattaro cewa, hukumar ta bugi ruwan cikinsa a binciken da ta ke yi na yadda aka karkakatar da biliyoyin kudade daga ma'aikatar sufurin jiragen sama
Ana zargin an bai wa Ahmad Sirika, kwangila na biliyan 8 ta kamfaninsa mai suna Engirios Nigeria Limited
Asali: Legit.ng