Home Back

‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

leadership.ng 2024/5/13
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

Akwai dai takun saka a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, biyo bayan barazanar ficewa daga jam’iyyar da ‘yan majalisar tarayya kusan 60 suka yi kan zargin jam’iyyar APC mai mulki ne ke kulawa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP.

Barazanar ‘yan majalisar dai ya biyo bayan nadin kwamitocin rikon kwarya na jam’iyyar PDP a Ribas da wasu jihohin kasar nan, wanda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar karkashin jagorancin Umar Damagum ya yi.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja, ‘yan majalisan sun bukaci a tsige Damagum daga mukaminsa na rikon kwarya na shugaban jam’iyyar PDP na kasa, inda suka yi gargadin cewa idan ba a yi haka ba, za su fice daga jam’iyyar.

Da suke magana kan zargin, masu magana da yawun gamayyar ‘yan majalisan dokokin na PDP, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere, Hon. Aliyu Mustapha (Kaduna), Hon. Awaji-Inombek Abiante (Ribas), Hon. Midala Balami (Borno) da wasu da dama, sun yi watsi da matakin mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, na neman murkushe magoya bayan PDP tare da fifita ‘yan jam’iyyar APC, musamman a Jihar Ribas.

A cewar ‘yan majalisan, za su taimaka wa mukaddashin shugaban wanda yake rike da mukamin ba bisa ka’ida ba, wajen ruguza jam’iyyar PDP idan har bai janye matakin ba tare da duba jerin sunayen kwamitocin riko na Jihar Ribas da sauran jihohi 16.

‘Yan majalisan sun kuma yi kira ga Damagum da ya yi murabus daga mukaminsa cikin gaggawa don ba da damar wani daga shiyyar Arewa ta tsakiya ya maye gurbinsa na kulawa da al’amuran jam’iyyar PDP bisa bin tsarin doka na ganin wani daga yankin Arewa ta tsakiya ya gaji tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da ya fito daga Jihar Benuwai, wanda aka tsige shi a ranar 28 ga Maris, 2023.

Sun sha alwashin taimaka wa Damagum wajen ruguza PDP idan ya ki cire ‘yan APC daga mambobin kwamitin riko na PDP a Ribas da wasu jihohi 16.

‘Yan majalisan sun dai zargi Damagun da nada ‘ya’yan jam’iyyar APC a cikin kwamitin riko na PDP na kananan hukumomi a Jihar Ribas da wasu jihohi da dama. Sun ce wannan mataki na iya kashe jam’iyyar PDP.

People are also reading