Home Back

Najeriya ta ce tana da maganin karancin abinci

dw.com 4 days ago
Kasuwar hatsi a arewacin Najeriya
Kasuwar hatsi a arewacin Najeriya

Ya zuwa yanzun dai farashin kowace lomar da ke ginin jiki a Tarayyar Najeriya dai ya karu da kusan kaso 32 cikin dari a watanni biyar na shekarar bana, a fadar hukumar kiddidigar kasar. Adadi mafi girma ga kasar da ta kalli hauhawar da babu irin ta cikin batun na cimaka a lokaci mai nisa. Tsada cikin batun na abinci ne dai yanzu haka ke zaman matsala ta kan gaba a zuciyar ‘yan mulkin Najeriyar.

Da suka kammala wani taro a Abuja sun ce suna shirin korar yunwa zuwa gidan tarihi a lokaci na kankane. Inuwa Yahaya dai na zaman gwamnan jihar Gombe kuma shugaban gwamnonin arewacin kasar.

"Mafi muhimmanci a gare mu shi ne yadda yanayin tsadar rayuwa musamman yunwa ke neman shiga cikin kasar nan. Tattaunawar da muka yi ta ta'allaka ne a kan ya za a habaka noma ta yadda za a samu yabanya a koma kamar yadda aka saba cikin wadata ta abinci da tattali na arziki."

Ko bayan jeri na agajin abinci, Abujar ta ce ta kaddamar da sayar da taki a jihohin Najeriyar 36, da ma taraktocin noma duk dai a kokari na sauya rayuwar ‘yan kasar da ke cikin halin yunwa. Masu mulkin dai sun kuma suna shirin kashe wasu tsabar kudi har Naira miliyan dubu 155 wajen sake sayen abinci da kai shi zuwa talakawa na kasar. Watan gobe na Yuli da ma dan uwa na Agustan da ke tafe dai na zaman watannin wahala cikin batun na abinci.

Sanata Abubakar Kyari dai na zaman ministan noman Tarayyar Najeriya da kuma ya ce kasar ta yi nisa cikin shirin kare yunwa a bana.

"Mun bai wa jihohi taki, mun ba su takin a kimanin buhu miliyan daya da dubu 100, suna dauka yanzu, amma mun ce su yi gaggawa domin yanzu ake bukatarsa. Kuma kwannan za mu tura ragowar kayan kamar maganin feshi da kuma na kashe ciyawa. Najeriya ta shirya tsaf wajen batu na abinci, sai dai kuma akwai matsalar tsadar taki, shi ma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa matakai, kwanan nan za a rage farashin taki."

Duk da cewar dai a mafi yawan sassa na kasar dai damina ta fara, batun farashin takin dai na zaman kalubale a tsakanin miliyoyi na manoma da kaiwa ya zuwan biya na bukata ta abincin. Buhun takin dai kan kai kusan Naira dubu 50 a kasar da masu noman ke kokawa cikin batu na ci da kai.

Mafita a cikin harkar noman a fadar Mohammed Magaji da ke zaman kakakin kungiyar manoma ta kasar na zaman kyautar takin maimakon saukin da masu mulkin suke kira a halin yanzu.

"Su gwamnatocin jihohin nan, takin da suka saya da wanda za su saya, su hada da wanda gwamnatin Tarayya ta ba su, su bai wa manoma kyauta. In an ba da shi walau 15, 15, walau NPK shi Urea ana iya barin sa sai nan gaba. In an yi haka to za a samu saukin noma, musamman a jihohin da ke da zaman lafiyar da za su samu damar noma."

Kiddidigar hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce akalla mutane miliyan 31 ne ke iya fuskantar mummunan karanci na abinci a tsakanin watan Yunin da ke shirin fita da Agustan jibi, a cikin Tarayyar Najeriya da a baya ke fadin ta darma sa a cikin batun na da‘ami.

People are also reading