Home Back

Ana Tsaka da Sarautar Kano, an Rasa Rai Bayan Miyagu Sun Yi Ta'asa, Sun Jikkata Ƴan Sanda

legit.ng 2024/10/5
  • Yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar Kano, wasu miyagu sun hallaka mutum daya da jikkata jami'an ƴan sanda
  • Miyagun sun yi ajalin mutumin mai suna Muktar Garba da aka fi sani da Babalia a yankin Jaen Makera da ke Kano
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka dage ci gaba da sauraran shari'ar da zuwa karfe biyu na ranar yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wasu miyagu a jihar Kano sun kai farmaki inda suka hallaka mutum daya da jikkata ƴan sanda biyu.

Lamarin ya faru ne a unguwar Jaen Makera da ke birnin Kano ana tsaka da shari'ar sarautar jihar.

Kwamishinan ƴan sanda, Hussaini Gumel shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 a Kano, cewar Premium Times.

Gumel ya ce miyagun sun yi ajalin wani mai suna Muktar Garba da aka sani da Babalia yayin ta'asar.

Kwamishinan ya ce Muktar ya rasu ne a asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya ce an mika gawar marigayin ga yan uwansa domin binne shi kamar yadda tsarin Musulunci ya koyar.

Wanann na zuwa ne yayin da ake tsaka da shari'ar sarautar jihar a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Kotun ta dage zaman zuwa karfe biyu na ranar yau Alhamis domin ci gaba da sauraran shari'ar tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading