Home Back

FARAUTAR YAHAYA BELLO: Kotu ta umarci EFCC su kai wa lauyan Bello sammacin bayyana a kotu

premiumtimesng.com 2024/5/12
SABUWAR RIGIMA A APC: Ba zan janye daga takara ba, zan ragargaza APC idan aka cire suna na -Yahaya Bello

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar EFCC ta aika wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello sammacin neman Naira biliyan 80 a wurin sa ta hannun lauyan sa.

A wani umarni da Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar a ranar Laraba, ya ce EFCC ta aika da sammacin ganin yadda Bello wanda ya ari takalmin kare ya falfala a guje, bai hallara a kotun ba, a ranar Talata ɗin.

Wannan ne karo na biyu da Yahaya Bello ya ƙi halartar zaman kotun da aka gayyace shi, domin EFCC ta gurfanar da shi.

Rashi halartar sa kotu ne ya kawo tsaikon shari’ar a ranar 18 ga Afrilu.

Tun a ranar 17 ga Afrilu ne dai kotu ta bada sammacin kamo Bello domin EFCC ta gabatar da shi a washegari 18 ga Afrilu, amma ‘yan sandan da ke gadin gidan sa a Abuja suka yi artabu da jami’an EFCC, har Gwamnan Kogi, Ododo wanda ya gaji Bello ya fice da shi a cikin motar sa.

Daga nan ne hukumomin gwamnatin tarayya su ka bayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo.

An dai yi artabu a gidan Yahaya Bello da ke Zone 4, Abuja.

A yau Talata sai Mai Shari’a ya umarci lauyan EFCC, Kemi Pinheiro ya aika sammacin neman Yahaya Bello ga lauyan sa, Abdulwahab Mohammed.

Nwete ya ce ya yi amfani da Doka ta Sashe na 382(4) da (5).

Bello Ya Nemi A Soke Neman Sa Ruwa Jallo Da Ake Yi:

Sai dai kuma jim kaɗan bayan kotu ta ce lauyan EFCC ya aika wa lauyan Yahaya Bello sammacin shi Bello ɗin, sai wani lauya ya miƙe a madadin Yahaya Bello ya nemi kotu ta soke farautar tsohon gwamnan da jami’an tsaro ke yi.

Lauyan mai suna Adeola Adedipe (SAN), ya ce a soke sammacin farauta Yahaya Bello, saboda mai shari’a ne da kan sa ya bayar da sammacin, ba wani ɓangare ne na masu shigar da ƙara suka nemi a bayyana sammacin farautar Bello ɗin ba.

People are also reading