Home Back

'Yan Majalisar Tarayya Sun Nemi a Kara Wa'adin Shugaban Ƙasa da Mulkin Karba-Karba

legit.ng 2024/7/6

FCT Abuja - Wasu mambobin majalisar wakilan tarayya na neman a yiwa kudin tsarin mulkin Najeriya 1999 garambawul domin a saka tsarin karɓa-karɓa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Tawagar ƴan majalisar sun bukaci haka domin a tsara yadda shiyyoyi shida na Najeriya za su riƙa karɓa-karba a kujerar shugaban ƙasa.

Har ila yau sun nemi a yi wa kundin tsarin mulki gyara domin ya tanadi “wa’adi guda na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnonin jihohin Najeriya.

Ɗan majalisa mai wakiltar Ideato ta Kudu da Arewa daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana hakana madadin ƴan majalisar ranar Litinin a Abuja.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading