Home Back

Rarara ya yi amfani da ni ne ya jefar, ya kama gaban sa – Zango

premiumtimesng.com 2024/5/4
Rarara ya yi amfani da ni ne ya jefar, ya kama gaban sa – Zango

Fitaccen jarumi Adam Zango ya bayyana cewa mawaki Dauda Kahutu da ake kira da Rarara ya yi amfani da shine ya sannan daga baya ya wancakalar da shi.

Zango a wata faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa yayin da yake bada amsa tambayar da aka yi masa kan alakar sa da mawaki Rarara, Zango ya ce, bai amfana da Rarara ba kamar yadda wasu mutane ke zato a farfajiyar Kannywood.

Zango ya ce ” Rarara ya yi amfani da ni mun yi tafiye tafiye na kamfen garuruwa sun fi bakwai, amma ina tabbatar muku cewa babu amfana da na yi da shi.

” Sai mu yi tafiya da Rarara ya samu miliyan sama da 100 amma idan muka dawo sai ya aika min da naira 250,000 ya ce a sha ruwa za a hadu. Duk da haka bai hana idan ya neme ni mu fita ba in bishi.

” ‘Kai dai ka ga Rarara kawai. Zai yi amfani da mutum ne idan ya samu abinda ya ke so sai ya yi watsi da kai ya kama gaban sa.

” Ku je ku tambayi abokanan sa irin su Baban Chinedu, za su faɗi muku.

People are also reading